TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA TARA (29)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 29

 

HAJJIN BANKWANA

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

A cikin Shekara ta 10 bayan Hijiran Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina, Annabi (SAW) yayi aikin Hajji na bankwana Wanda daga wannan hajjin Bai sake yin wani aikin Hajji ba (kuma kafin wannan ma baiyi wani aikin Hajji ba).

 

Kimanin Musulmai Dubu Chasa’in 90,000 ne sukayi wannan Hajjin tare da Annabi Muhammad (SAW), A ranar yanka Ma’ana ranar Sallan Laiha, Annabi Muhammad (SAW) yayi Huduba Wanda yayi bankwana wa mutanen Duniya Baki daya.

 

A cikin Hudubarsa ta bankwana, Annabi Muhammad (SAW) ya Bayyana Asalin Ma’anar Addinin Musulunci, Abunda ya kunsa na Ibada da Mu’amala.

 

Ciki harda fadinsa cewa: Haramun ne Kashe Ɗan Adam, kwace masa Dukiya ko wani abu daya Mallaka. Yace kuma, Musani cewa Matanmu sunada Hakki a kanmu, muma munada Hakki a Kansu, Musulmai ƴan uwan juna ne, Dukiyar Musulmi bata halatta ga waninsa Saida Amincewar Mai Dukiyar.

 

Annabi Muhammad (SAW) yace: Musani cewa Daukanmu daga Annabi Adam (A.S) muke, shikuma Annabi Adam (A.S) daga Ƙasa Allah ya halicceshi. Bawanda yafi wani girma a wajen Allah (SWT) sai Wanda yafi wani Tsoron Allah, Balarabe baifi bakar fata a wajen Allah ba, sai dai Idan yafishi tsoron Allah.

 

Wannan kadan daga cikin Hudubar tasa Kenan ta bankwana. insha’Allah zan kawo muku fassarar Hudubar nan gaba kadan Idan na gama Wannan tarihi.

 

Allah ya taimakemu ya biya mana bukatunmu Alfarman Annabi Muhammad (SAW). Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button