TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA BAKWAI (7)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 7

 

TAFIYARSA (SAW) ZUWA SHAAM (Syria)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Yanada Shekaru 18 a rayuwarsa ta Duniya Baffansa Abu-Talib yayi tafiya dashi zuwa sham domin Kasuwanci, yayinda suka isa ‘Busra’ Wani Malamin Yahudawa mai suna ‘Bahira’ ya kalli Annabi Muhammad (SAW) sai yayiwa Baffansa Abu-Talib isahara da yakoma dashi gida (Makka), domin Karda Yahudawa suganshi zasu cutar dashi. Ya kuma bawa Baffansa Abu-Talib labarin cewa wannan Matashin (Annabi SAW) zai Zama wanni Babban Mutum nan gaba, dajin haka sai suka koma gida (Makkah).

 

Yana da Shekaru 25 Annabi (SAW), sai Sayyada Khadijatu Bintu Khuwailid taji labarin Aminci, Amana da Gaskiyar Annabi Muhammad SAW, sai taso suyi kasuwanci tare. Da sukayi kasuwanci sai akasamu ribar da ba’a taba samu bah Albarkacin Annabi Muhammad (SAW).

 

Sunyi tafiyar tareda wani bawanta ‘Maisarah’ Wanda Sayyada Khadijah tasa shi ya dinga kula da duk abunda ya faru ya kawo mata labari. ‘Maisarah’ yana Kula da irin Mu’ujizozin dake faruwa da Annabi Muhammad (SAW) yayin tafiyar tasu. Da suka dawo da riba mai yawa kuma bawanta yabata labarin abubuwan Al’ajabi dasuka faru yayin tafiyar, (Yace mata idan muna tafiya girgijen yake masa inuwa, Idan ya taka kasa (Yashi) zanen ƙafarsa baya fitowa amma idan ya taka dutse sai tafin ƙafarsa ya Bayyana, yace mata da mukaje Layi akayi wajen sayan kayan da Annabi Muhammad (SAW) yaje dashi, saida nashi ya ƙare aka fara sayan na sauran mutane, da sauransu). Sai Sayyada Khadijatul Kubra taji So da Kaunar Annabi Muhammad (SAW) ya kara shiga zuciyarta, sai ta nemi Auren Annabi Muhammad (SAW)

 

Ya Allah Albarkacin wannan tafiyar ka kiyaye mana hanyoyin mu, kasa duk inda zamuje muje lafiya mu dawo lafiya. Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button