TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA BIYAR (5)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 5

 

TASHIN (girman) ANNABI (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Annabi Muhammad (SAW) ya tashi yasamu mahaifinsa ya rasu a Madina kafin haihuwarsa, kuma mahaifinsa Sayyidina Abdullahi baibar masa dukiya Mai tarin yawa bah. Yana Dan Shekara Shida (6) mahaifiyarsa Sayyada Aminatu ta rasu a hanyar Dawowa daga Madina sai aka bunneta a wani gari ‘Abwa’a’ (garine tsakanin Makka da Madina).

 

Kakansa Abdul-Mutallib shi yaci gaba da renonsa da kulawa dashi, Abdul-Mutallib yana son Annabi Muhammad (SAW) sosai tsabar so da kulawa da yakewa Annabi (SAW) duk inda zaije tare suke zuwa, bayan shekara biyu (2) Allah yayiwa Abdul-Mutallib Rasuwa Annabi (SAW) nada Shekaru Takwas (8).

 

Banyan rasuwar Kakansa Baffansa Abu-Talib (Baban Sayyidina Ali RTA) ne yaci gaba da Kula dashi. Abu-Talib ya kasance ba mai yawaitar Dukiya bane Amma saboda daukan reno da kulawa da yayi na Annabi (SAW), Allah ya yawaita masa Arzikinsa, yasamu Akhairai da yawa.

 

Muna Tawassuli da Annabin Rahama (SAW) Allah ya yawaita mana Akhairai Duniya da Lahira. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button