TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA BIYU (2)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 2

 

NASABAR ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Kaman yadda mukayi bayani Kan tsatson Annabi (SAW) cewa yafito daga tsaron Larabawa Kabilar Quraish, ga Jerin sunayen gwarazan iyaye, Kakanin Sayyidina Rasullallahi (SAW), mutanen kirki wanda ba’a taɓa yiwa wani daga cikinsu shaidar Zina, shan giya, chacha, ko Sata ba.

 

Sunansa Muhammadu (SAW) Dan Abdullahi Dan Abdul-Mutallib Dan Hashim Dan Abdul-Manaf Dan Qusaiy Dan Kilaab wato Hakim, Dan Murrarah Dan Ka’ab Dan Lu’aiy Dan Ghaalib Dan Fihr Dan Maalik Dan Nadhri Dan Kinanah Dan Khuzaimata Dan Mudrikata Dan Ilyasa Dan Midhara Dan Nizaari Dan Ma’addi Dan Adnaani wanda Nasabarsa take zuwaga Annabi Isma’il (AS) Dan Kalilullah Annabi Ibrahim (AS).

 

Mahaifiyarsa kuma Sunanta Amina ‘yar Wahab Dan Abdul-Manaf Dan Zuhrata Dan Kilaab Wato Hakim, Kakan Annabi Muhammad (SAW) na Biyar Kenan.

 

Shi Annabi (SAW) yakasance tsarkakakke ne a Nasabarsa kaman yadda Hadisi ya tabbatar, kuma Nasabar Mahaifinsa Abdullahi da Mahaifinsa Amintu na Haduwa ne Kan Kakansa na Biyar har yaje izuwa Khalilullah Annabi Ibrahim (AS).

 

Allah ya bamu Albarkacin wadannan bayin Allah dasuka dauki sirrin Haske da haihuwar Annabi (SAW) tun daga Annabi Adamu (AS) har Kan Mahaifinsa Sayyidina Abdullahi da Mahaifiyarsa Sayyidatuna Aminatu. Amin.

 

07032509197

  1. yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button