TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA DAYA (1)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 1

 

TSATSON ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Shi Annabi Muhammadu SAW ya kasance tsatso na Qabilar Larabawa dake Makka wato ‘Quraish’ sune qabila mafi daukaka cikin Larabawa, sun shahara fagen Ilimi da hikima, Jarumta, da girma da girmama mutane.

 

Quraish sun kasance ma’abota Kasuwanci, saukan Baki, dama kulada Dakin Ka’abah. Quraish nada mukami Mai girma cikin Larabawa.

 

Quraishawa sune qabila mafi girma da mutunci da garin Makka, sunfi kowace qabila daraja, ƙima, martaba, da mutumta Al’ummar garin maka da baƙin dake zuwa garin. An sansu da gaskiya, Amana, hakuri, juriya, da rashin shiga ayyuka na jahilci, koda cewa kafin Haihuwar Annabi Muhammad (SAW) Lokacin Jahiliyya ne.

 

Yayin da aka Shugabantar da Qusaiy Ibn Kilab a Makka domin kulada Dakin Ka’abah, biyo bayansa sai Hashimu Ibn Abdul-Manaf ya shahara bayanshi kuma sai Abdul-Mutallib Ibn Hashim Kakan Annabi Muhammad (SAW) sai ya zama sune ke kula da Dakin Ka’abah.

 

Allah ya bamu Albarkacin Quraishawa domin martaban Ɗan da ya fito cikinsu (Annabi Muhammad SAW) Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button