TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA (10)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 10

 

DA’AWAR ANNABI MUHAMMAD (SAW) CIKIN SIRRI.

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Yayinda Allah yai masa wahayi cikin Suratul Muddassir “Tashi Kayi Wa’azi…” A wata Ayar kuma Allah yace masa “Ka gargaɗi Danginka makusanta…” Sai Annabi Muhammad (SAW) ya fara kira zuwaga Allah cikin sirri ya fara a iyalansa da wasu daga cikin Abokansa.

 

Wanda ya fara Musulunta cikin Maza shine Sayyidina Abubakar, A Yara Maza kuma Sayyidina Ali bin Abi-Talib, a Mata Sayyada Khadijatul Kubra Matar Annabi Muhammad (SAW), a bayi kuma Sayyidina Bilal(Allah ya kara musu yarda)

 

Sayyidina Abubakar yayi kira ga Abokansa domin Shiga Addinin Musulunci, dayawa daga cikinsu sun amsa masa. Daga cikin harda Sayyidina Usman bin Affan, Zubair Bin Auwam, Abdulrahman Bin Auf, Sa’adu Bin Abi-waqqas da sauransu.

 

Haka Annabi Muhammad (SAW) yacigaba da Kira cikin sirri wa Danginsa da Abokansa har na tsawon shekaru 3 Yana Da’awar, Sai Allah yai masa izini daya bayyana Da’awar Addinin Musulunci.

 

Muna Tawassuli da Kiran da Annabin Rahama (SAW) yayi, da Imani sahabbai Allah ya Kara mana shiriya da Imani. Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button