TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA BAKWAI (17)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 17

 

MUBAYA’AR MUTANEN MADINA A KARO NA BIYU

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Wadanda suka Musulunta daga mutanen Madina Basu gushe ba suna Kiran Yan uwansu zuwaga Addinin Musulunci har sai da wasu dayawa suka Musulunta a Madina.

 

A karo na biyu, Musulmai 75 ne daga Madina sukayiwa Annabi Muhammad (SAW) Mubaya’a 73 Maza, Mata 2. Sunyi Imani da Allah SWT dakuma yin Alqawarin cewa zasu kareshi daga Sharri da cutarwan Kafiren Makka. Sun bukaci Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa dasu kauro Madina zasu basu Kariya.

 

Bayan komawarasu Madina dayawa daga cikin Sahabban Annabi Muhammad (SAW) sun bisu Madina suka tare a Madina Baki daya, sai ya kasance Annabi Muhammad (SAW) da wasu kadan daga cikin Sahabbai ne suke Makkka. Awannan lukacin wasu Sahabban Annabi Muhammad (SAW) kuma suna Habasha.

 

Haka akaci gaba da kira zuwaga Addinin Musulunci a Makka da Madina Baki daya.

 

Allah ya kara daukaka Addinin Musulunci da Musulmai Allah ƙasƙantarda Kafurci da kafurai aduk inda suke. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button