TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA BIYAR (15)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 15
TAFIYAR ANNABI MUHAMMAD (SAW) ZUWA ‘DA’IFAH
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Bayan Wafatin Matarsa Sayyada Khadija wacce take taimaka masa da Dukiyarka da shawarwari masu kyau domin cigaban Addinin Musulunci, dakuma Rasuwar Baffansa Abu-Talib wanda shine Mai kareshi daga cutarwar Kafiren Makka, sai cutarwar tayi tsanani sosai domin yanzu babu Wanda zai tsaya masa. Ganin haka sai Annabi Muhammad (SAW) ya fita zuwa ‘Da’ifah.
Annabi Muhammad (SAW) yaje ‘Da’ifah tare da Zaidu Bin Harisata. Da isar Annabi Muhammad (SAW) Garin ‘Da’ifah, ya kirasu zuwa ga Addinin Musulunci yakuma nemi suyi Imani da Allah, su bashi Kariya daga cutarwar Kafiren Makka. Bayan haka yakuma nemi da zai zauna tare dasu, domin ficewa daga wahalar da Musulmai Kesha a Makka.
Mutanen ‘Da’ifah sunyi watsi da Kiran Annabi Muhammad (SAW) suka kuma Walakantashi. Sukasa bayinsu da ‘yan iskan garin ‘Da’ifah sukata Zagin Annabi Muhammad (SAW) harda Jifan Annabi Muhammad (SAW) da Duwarwatsu. Innalillahi Wa’innan Ilaihir-Raji’un!!! _”Inama ace inanan Lokacin in bada rayuwata domin kare Annabi Muhammad (SAW)”_
Sunyita Jifan Annabi Muhammad (SAW) har sukaji masa raunuka, jini na fita daga jikin Annabi Muhammad (SAW). Mala’ika yazo masa Yana butakar Annabi yayi izini a hallaka mutanen garin, Amma Annabi SAW yace “Allah ka shirya mutanena domin basusan wayeniba”.
Wannan duk yafarune a shekara ta 10 bayan Aiken Annabin Rahama (SAW). A hanyarsa ya hadu da Aljanu 8 wadanda suka Musulunta.
Ya Allah Ka daukaka Addinin Musulunci a dukkan fadin Duniya, Allah kaga bayan duk Wanda ke cutar da Musulmai da Musulunci. Amin.
07032509197
yaseen9253@gmail.com