TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA BIYU (12)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 12

 

HIJIRAN FARKO; ZUWA HABASHA

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Cikin Shekara ta 5 bayan Aiko Annabi Muhammad (SAW), yayinda Kafuren Makka sukaga Addinin Musulunci ya fara daukaka bayan Musuluntar Sayyidina Hamza da Sayyidina Umar. Sai kafiren Makkah sukaga cewa yanzu bazasu iya cutar da Annabi Muhammad (SAW) cikin sauki ba, sai suka fara cutar da Sahabbansa musamman wadanda ba ‘ya’yan manya ba (Bayi da Marasa karfi). ganin haka sai Annabi Muhammad (SAW) yayi musu izini dasuyi Hijra zuwa Habasha.

 

Sahabban Annabi Muhammad (SAW) 12 ne Maza da Mata 4 sukayi Hijirar Farko zuwa Habasha, cikin su harda Sayyidina Usman bin Affan, da Matarsa Sayyidatuna Rukiyyah ‘yar Annabi Muhammad (SAW). Sunyi tafiyar Hijirar daga Makka zuwa Habasha.

 

Sarkin Habasha na Lokacin Najashi mutumin kirki ne, mai Adalci, son mutane da son Zaman Lafiya. Ya karbesu hanu bibbiyu yakuma Kula dasu batare da cutar dasu ko Bari wani Abu ya cutar dasu ba.

 

Allah domin wannan Hijirar da Sahabbai sukayi Kasa mu samu saukin wahalar damuke ciki kabamu lafiya da Zaman Lafiya Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button