TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA DAYA (11)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 11

 

BAYYANA DA’AWAR ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Bayan Allah (SWT) yayiwa Annabi Muhammad (SAW) irizini daya kirayi Danginsa Makusanta daga Farko, kafin ya bayyana Da’awar Addinin Musulunci. Cikin Shekara ta Uku 3 (Bayan Aike) Allah (SWT) yayi masa izini cewa ya bayyana Da’awar Addinin Musulunci ga daukacin Al’ummar Duniya baki daya.

 

Annabi Muhammad (SAW) ya bayyana Da’awarsa yakira Quraishawa zuwa ga kadaita Allah (SWT) dasu daina Bautar Gumaka, su daina Bautar abubuwan da bazasu amfanesu Duniya da Lahira ba, suzo zuwaga Halal subar Haram, subar Ayyukan Sharri suyi ayyukan Alheri. Daga cikinsu wasu sunyi Imani dashi wasu kuma sunqishi, sunyi Kiyayya, gaba dashi, sun kuma cutar dashi. A daga cikin manyan kafiren Makka wanda suka cutar da Annabi Muhammad (SAW) ya haɗa da; Baffansa Abu-Lahab Abu-Jahal da sauransu.

 

Annabi Muhammad (SAW) yacigaba da jure walaharwa, cutarwa makircin da sukayita masa, yacigaba da Kiran Al’ummah zuwa ga Allah (SWT) har Lokacin da yayiwa Sahabbai izini dasuyi Hijra zuwa Habasha (Wannan itace Hijira ta Farko) kafin ayi ta biyu zuwa Habasha kumadu, sai hijirar karshe zuwa Madina, wanda insha Allah a cikin wannan aikin namu kafin karshen watannan mai Albarka zan kawo muku tarihin yadda akayi su.

 

Allah ya tabbatar damu cikin so da kaunar Annabi Muhammad (SAW) na gaskiya. Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button