TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA HUDU (14)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 14.

 

RASUWAR MATARSA (KHADIJA) DA BAFFANSA (ABI-TALIB).

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

A shekara ta 10 bayan Aiken Annabin Rahama (SAW), Qabilu 5 na Quraishawa suka yanke hukuncin janye alqawarin da sukayi na sanyawa Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa Takunkumi. Yayinda Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa suka fita daga Takunkumin da suke ciki na Kimanin Shekaru 3, (Abinci ko wani abun more rayuwa baya zuwa musu, har Saida suka Fara cin ganyayen bishiya.) Subhanallah!. A Wannan Lokacin Shekarun Annabi Muhammad (SAW) 49 wasu sunce 48.

 

Bayan fitarsu daga wannan Takunkumin da watanni, Baffansa Abi-Talib (Baban Sayyidina Ali RTA) wanda shine mai kare Annabi Muhammad (SAW) daga cutarwan kafiren Makka yarasu, bada jimawaba Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra wacce take hidima da dukkanin abunda ta mallaka na dukiya, shawari da hikimomi wajen daukaka Addinin Musulunci itama tayi Wafati. Annabi Muhammad (SAW) yayi jimami kwarai da gaske na rashinsu domin irin gudumawar dasuke bayarwa wajen daukaka Addinin Musulunci, Har yakirayi wannan Shekarar da Aamul-Huzni (Shekarar Bakin Ciki).

 

Jim kadan bayan Rasuwar Baffansa da Matarsa, sai cutarwar Kafiren Makka yayi yawa gareshi, Wanda hakan Shi yajawo fitarsa zuwa Garin ‘Da’ifah.

 

Allah muna rokonka kabamu juriya, musamu nasara Kan dukkanin jarabawar daka jarrabemu. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button