TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA SHIDA (16)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 16

 

MUBAYA’AR FARKO TA MUTANEN MADINA.

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

A cikin Shekara ta 12 bayan Aiko Annabi Muhammad (SAW) Mutane 12 daga Madina suka hadu da Annabi Muhammad (SAW) a wajen (Aqabatul Ula) Aqaba ta Farko a Ranakun Mina.

 

Wannan mutane 12 daga Madina sun yiwa Annabi Muhammad (SAW) mubaya’a suka musulunta, sukayi masa Alqawari cewa bazasu hada Allah (SWT) da kowaba, bazasuyi Sata ko Zina ba, da Sauran munanan ayyuka na zunubi duk bazasuyi ba. Sun Musulunta kuma zasuyi aiki irin na Musulunci koda hakan zai jawo rasa rayukansu ne, sun yarda suna tare da Annabi Muhammad (SAW) duk rintsi duk wuya.

 

Yayinda zasu koma Madina, Annabi Muhammad (SAW) ya hadasu da Sahabinsa dazai cigaba da koyar dasu Alqur’ani Maigirma da Sauran abubuwan da suka shafi Addini. Haka sukaci gaba da kiran Yan uwansu zuwa ga Addinin Musulunci a Madina, Annabi Muhammad (SAW) kuma yana Makkah, shina yanata kiran mutane zuwa ga Addinin Musulunci.

 

Daga wannan lokacin ne hasken Addinin Musulunci ya fara haska garuruwa, musulunci ya ratsa zukatan mutane daga Qabilu daban daban.

 

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai, Allah ya ƙasƙanta Kafurci da kafurai aduk inda suka kasance. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button