TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA GOMA SHA UKU (13)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 13
HIJIRA NA BIYU ZUWA HABASHA.
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Yayinda Kafuren Makka suka Kara tsananta cutarwa ga Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa, sai Annabi Muhammad (SAW) ya sake yiwa Sahabbai umarni dasu kara yin Hijra zuwa Habasha (a Karo na biyu).
Sahabban Manzon Allah (SAW) Maza 83 ne da Mata 18 sukayi hijira a karo na biyu zuwa Habasha, daga cikinsu harda Ja’af Bin Abi-Talib. Sarkin Habasha Najashi ya karramasu ya kuma karbesu cikin mutuntawa.
Yayinda Kafuren Makka sukaji labarin hijirar dasukayi sai tura Amr bin Al-As da Abdullahi bin Zubair Al-Makzumiy da tarin kyauta su kaiwa Sarki Najashi domin ya kori Musulmai daga garinsa, kuma ya basu musulmai domin su dawo dasu Makkah zu azabtar dasu su kashesu. Sarki Najashi yaƙi karban Kyautar nasu, yakuma ƙi ya bari su tafida Sahabban Annabi Muhammad (SAW) bai basu damar cutar da Sahabbai ba.
Ganin haka sai suka Kara matsa lamba wajen cutar da Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbai a Makka, har takaiga sun yanke duk wata alaƙa da duk Wanda ya Musulunta, ba’a sayar musu da Abinci, ba’ayin duk wani abu dasu a Makkah, sukace indai anaso su janye wannan cutarwar dasukewa Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbai sai an Sallamar musu da Annabi Muhammad (SAW) sun kasheshi. (Subhanallah). Dukkanin Qabilar dake Makka sun yarda da wannan ƙudurin suka rubuta suka rataye a Dakin Ka’abah.
Wannan duk ya farune a shekara na 9 bayan Aiko Annabi Muhammad (SAW). Allah Ka dauke mana dukkanin wahalar damuke ciki zahiri da boye, Alfarman Annabi Muhammad (SAW). Amin
07032509197
yaseen9253@gmail.com