TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA HUDU (4)
TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 4
SHAYARWA DA RENONSA (SAW)
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Mahaifiyarsa Sayyada Aminatu ta shayar dashi na tsawon kwanaki, sai kuma Suwaibah baiwar Baffansa Abu-Lahab, sannan suka Sama masa Mai shayarwa kaman yadda Al’adar Larabawa take wajen shayarwa.
Halimatus-Sadiya itace ta karbi shayar da Annabin Rahama (SAW) zuwa garinta domin ya samu fasaha da dabarbaru na mutanen kwauye.
Garin da Halimatus-Sadiya take garine Mai karancin abubuwan more rayuwa da Albarka na kayan Noma, Kiwo da Kasuwanci, Albarkacin daukan Annabi Muhammad (SAW) da Halimatus-Sadiya tayi zuwa wannan garin, Allah ya saukar da Albarka Mai yawa a garin, suka samu Albarka da Arziki Mai yawa sosai.
Halimatus-Sadiya Ta shayar dashi tsawon Shekaru biyu, sai ta nemi Alfarma wajen Mahaifiyarsa Sayyida Aminatu cewa tanaso Annabi (SAW) yacigaba da Zama a wajenta, domin irin abunda ta gani tare dashi na Albarka da falala. Sayyada Aminatu ta amince Mata, ya Kara Shekaru biyu a wajen Halimatus-Sadiya. Yanada Shekaru Hudu (4) Halimatus-Sadiya ta Mayar dashi wajen Mahaifiyarsa Sayyada Aminatu.
Allah muna tawassuli da Annabinka (SAW) ka nama Fatahi na dukkanin Albarka zahiri da baɗini. Amin.
07032509197
yaseen9253@gmail.com