TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA SHIDA (6)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 6
TARIHINSA (SAW) KAFIN ANNABTA
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Annabi Muhammad (SAW) kafin Annabta yayi fice cikin matane da Gaskiya, ƙasƙan da kai, da Riƙon Amana da mutunta mutane. Mutane sun kasance suna bawa Annabi Muhammad (SAW) kuɗaɗe da kadarorinsu domin ya ajiye musu saboda Amanarsa. Tsagwarar Amanarsa ce tasa suka saka masa suna ‘Al-Amin’ “Amintacce”.
Shi Annabi Muhammad (SAW) bai taba Shan giya ba, bai taba bautar gunki ba, bai taba caca, ko Zina ba, Annabi Muhammad (SAW) baitaba sabawa Allah ba ta kowani irin fanni.
Yanada Shekaru 35 a rayuwarsa ta Duniya quraishawa suka sabunta ginin Dakin Ka’abah, sai sukayi jayayya Kan Wanda zai maida ‘Hajarul-Aswad’ inda yake yanzu, sai sukace toh mu dakata duk wanda ya fara ɓullowa shine zai raba mana gardama, suna tsaye sai Annabin Rahama (SAW) a ɓullo, sai sukayi maraba da Zuwansa domin sanin Halayyansa kyawawa, suka fada masa abinda suke ciki suka nemi ya raba musu gardama, sai Annabi Muhammad (SAW) sai ya shinfida Mayafinsa ya daura ‘Hajarul-Aswad’ akai, sai yace Shugaban kowace Qabila ya kama gefen Mayafin, sai aka daga, da aka isa wajen da za’a ajiye ‘Hajarul Aswad’ ɗin sai Annabi Muhammad (SAW) yasa hanunsa mai Albarka ya dauki Hajarul-Aswad aje a wajen da yake yau. Shikenan ya raba fada, su kayi farin ciki sosai domin ganin yadda Annabi Muhammad (SAW) yayi musu Adalci.
Haka Annabi Muhammad (SAW) ya kasance kafin Annabta da halaye masu matuƙar kyau. Allah ya bamu ikon yin koyi da wadannan halayya masu kyau Alfarman Annabi Muhammad (SAW). Amin.
07032509197
yaseen9253@gmail.com