TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA TALATIN (30)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 30

 

RASHIN LAFIYAR ANNABI (SAW) NA KARSHE A DUNIYA.

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Bayan Hajjin bankwana, Annabi Muhammad (SAW) yayi wani Rashin lafiya Mai tsanani, Rashin Lafiyan yafarane tun karshen watan Safar, yayinda Rashin Lafiyan yayi tsanani sai yanemi izini wajen dukkanin Matansa cewa su yarda yayi Jinya a Dakin matarsa Sayyada Aisha, nan take suka yarje masa.

 

Yayinda Rashin Lafiyar Ma’aiki (SAW) tayi tsanani, har takai ga baya iya fita waje, sai yayiwa Babban Sahabbinsa, Masoyinsa, Mai Gaskiya abun gaskatawa, wato Sayyidina Abubakar izini cewa ya Shugabanci mutane a Sallah.

 

Kudubar da Annabi Muhammad (SAW) yayi ta Karshe itace wacce yayi Lokacin da Ansar (Musulman Madina) sukaji labarin tsananin Rashin Lafiya da yake fama dashi. Ansar sun taru a Masallacin Annabi Muhammad (SAW) har saida Annabi Muhammad (SAW) ya fito Sayyidina Ali, Fadl da Sayyidina Abbas suna rike dashi Yana Dogarawa dasu, suka zaunar dashi Akan Minbari.

 

Annabi Muhammad (SAW) yayi musu Kuduba wanda yawaicu jawaban dake cikinta kirane ga Al’ummah dasu Zama masu tawakkali ga Allah (SWT), su dinga Tina Allah a dukkanin abubuwan da sukeyi, kuma su tuna cewa komai yayi farko zaiyi karshe.

 

Ciki Hudubar harda fadinsa cewa: “Yaku mutane labari ya isomun cewa kuna tsoron mutuwar Annabinku, shin Annabawa kafin ni (Annabi Muhammad SAW) sun Dauwama ne? Kusani kaman Yadda Allah ya dauki rayukansu Nima Allah zai dauki raina. Yaku mutane kusani cewa bawani waje zanje ba, face zan hadu da Ubangiji na, nan bada jimawaba kuma zaku hadu Dani, Ina muku wasiyyah da Kuyiwa Muhajirun Alheri, kuma Muhajirun Kuyiwa Ansar Alheri…”

 

Wannan kadan ne daga Jawabinsa (Khuduba) da yayiwa Sahabbai a Karshen rayuwarsa. Allah ya Kara mana Kaunar Annabi Muhammad (SAW) da koyi dashi cikin zancenmu da Ayyukanmu. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button