TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA TALATIN DA DAYA (31)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 31

 

WAFATIN ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Annabi Muhammad (SAW) yayi Wafati bayan Jinya da yayi fama da ita. Da Jin Labarin Wafatin Annabi Muhammad (SAW), Sahabbai sukayi dafifi a Kofar gidansa domin Hali da suka Shiga na Jimami inda wasu daga cikinsu Basu yarda akan cewa yayi Wafati ba.

 

Sayyidina Umar (RTA) na cikin Wadanda Basu yarda cewa Annabi Muhammad (SAW) yayi Wafati ba a wannan lokacin. Dajin labarin Wafatin Annabi Muhammad (SAW), ya fitar da takobinsa cewa sai ya sare kan duk wanda kecewa Annabi Muhammad (SAW) yayi Wafati mutane su daina faɗan haka karya suke (shin Sayyidina Umar bai yarda ba)

 

A Wannan Lokaci Sayyidina Abubakar baya kusa. Amma dajin labarin Wafatin Annabi Muhammad (SAW), sai ya garzayo izuwa Gidan Annabi Muhammad (SAW) domin ya tabbatar. Dazuwansa Ya Shiga Gidan Annabi Muhammad (SAW) ya tabbatar da Wafatin nasa yayi kuka kwarai da gaske domin Rashin Masoyinsa, sai ya fito waje domin yayiwa Al’ummah jawabi.

 

Da fitowarsa ya hau kan minbari, yayi jawabi; ga kadan daga cikin Jawabinsa: Sayyidina Abubakar yace “Lallai wanda yakasance Annabi Muhammad (SAW) yake bautawa to Hakika Annabi Muhammad (SAW) yayi Wafati, Wanda yakasance yana bautawa Allah (SWT) ne kuma, to Allah Rayayye ne baya Mutuwa. Ya karanta wannan Ayar daga Alqur’ani Maigirma _’Annabi Muhammadu baikasance ba sai dai Annabi da Annabawa suka wuce kafinsa, Idan yayi Wafati ko aka kasheshi sai kujuya baya zuwa ga Kafurcinku nada, Wanda ya juya baya bazai cutar Allah da komai ba, da sannu Allah zai sakawa Masu gode masa'”_.

 

Annabi Muhammad (SAW) yayi Wafati ranar Litinin 12 ga watan Rabi’ul Auwal Shekara ta 11 bayan Hijira. Yayi Wafati yanda Shekara 63.

 

Alqawarin Allah ne dukkan Mai rai za’a wayi gari watarana babu shi, mu mun yarda Annabi Muhammad (SAW) yana Raye Amma a cikin zukatanmu. Allah ya Kara mana Kaunarsa da bin koyarwansa. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button