TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA TARA (9)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 9

 

FARKON ANNABTAR ANNABI MUHAMMAD SAW (Aikoshi a Matsayin Annabi da Wahayin Farko)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Yayinda Annabi Muhammad (SAW) ya kusanci Shekara 40 sai ya yanke saduwa da mutane ya kasance yana Keɓewa yana bautar Allah (Halwa) a Kogon Hira. Wani Lokaci Yana Kwana goma zuwa wata daya a cikin kogon hira tun kafin a aikoshi a matsayin Manzo a cikin kogon yana ibada, duk sanda ya fito sai ya koma gida wajen Matarsa Sayyidatuna Khadijatul Kubra domin ya karbo Abinci, idan ya karɓa Abinci sai ya kara komawa Kogon Hira ya cigaba da Ibada. kuma Sayyidatuna Khadijah bata taɓa kosawa ko gajiya da hakan ba, haka Annabi Muhammad (SAW) yakasance cikin bautar Allah har Allah ya Aikoshi a Matsayin Annabi. (Wahayi na farko ya sauka masa).

 

Yayinda yakai Shekaru 40, sai Mala’ika Jibrilu yazo masa ya sameshi a kogon hira Yana ta bautar Allah, sai yace Masa “Iqra’a” (Yikaratu) ya fada masa sau uku, Annabi Muhammad (SAW) yana mayar masa da Amsar cewa “Ma ana bi Qari’in” ma’ana “Ni bamai karatu bane”. Sai ya saukar masa Ayoyi biyar da farkon Suratul Alaq.

 

Bayan nan, sai Annabi Muhammad (SAW) ya koma gida wajen Matarsa Sayyada Khadijatul Kubra ya fada Mata abunda yafaru, Zuciyarsa na tuna ganin Mala’ika Jibrilu yadayi. Sai Matarsa Sayyida Khadijatul Kubra tace tana tsammanin wannan Mala’ika ne Wanda yake kawo sakon Allah zuwa ga Annabawa. Daga wannan Wahayin Annabi Muhammad (SAW) yacigaba da karban wahayi na Alqur’ani Maigirma daga wajen Mala’ika Jibrilu.

 

Allah ya bamu Albarkacin Alqur’ani Maigirma yakuma samu muyi koyi da koyarwansa. Allah Kasa Alqur’ani ya cecemu. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button