TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA UKU (3)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 3

 

HAIHUWAR ANNABI MUHAMMAD (SAW)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

An haifi Annabi Muhammad (SAW) a Makka ranar Litinin Shabiyu (12) ga watan Rabi’il-Auwal a shekarar yakin Giwa.

 

Ana Kiran shekarar da Shekarar yakin Giwaye ne (Aamul-Feeli) domin a shekarar ne Sarkin Habasha Mai suna Abrahata ya aika da runduna daga Habasha zuwa Makkah, cikin Rundunar harda Giwaye domin rusa Dakin Ka’abah, Amma Allah (SWT)ya hallakasu Baki dayansu da Giwayen nasu, ya sanya Kaidin su cikin bata, domin ya nuna martaban ɗakinsa. (Kaduba Tafsirin Suratul Feeli zakaga karin bayani).

 

Wannan shine yasa Larabawa ke cewa shekarar ‘Shekarar yakin Giwaye’ (Aamul-Feeli) kuma suke Lissafi da ita. Domin irin abunda ya faru a shekarar bai taba faruwa ba a tarihin Duniya. Allah ya tsara haka ne domin shekarar da Shugaban Halittun Allah baki ɗaya zai sauko Duniya ta zama shekarar da baza’a taɓa mantawa da ita ba. Alhamdulillah.

 

Sayyidatuna Aminatu tace bata taɓa jin wani ciwo ko yin rashin lafiya irin na laulayin ciki ba, kuma wajen haihuwarsa (SAW) bataji wani zafi ko raɗaɗaɗin haihuwa ba, Allah ya sauwaqe mata komai domin Alfarman wanda yake cikin ta (SAW).

 

Rahamar Allah ta sauka. Allah muna tawassuli da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) Ka Shirya Al’ummah musulmai Baki daya Manya da Yara Maza da Mata. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button