Tarihin Rayuwar Sheikh Adamu Kontagora RA

SHEKARU ASHIRIN (20) DA WAFATIN MAULANMU SHEHU ADAMU KONTAGORA (R.T.A) 1916-2003 AD

 

 

Shehu Adamu Haruna ɗan Sayyida A’isha, ya ƙare rayuwar sa ne kaf a cikin hidimar Allah da Manzon sa Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama.

 

Tun bayan haihuwar sa a shekaran 1344AH, wato 1916 AD, a garin Kotonkoro ƙaramar hukumar Bangi, Sheikh Adam ya fara karatu a gaban mahaifin sa Mallam Haruna, da kuma babban wan su Malam Muhammadu Dan Idi.

 

Bayan Shehu ya fara tasawa sai ya tattara ya bar gida ya tafi garuruwa daban-daban domin neman ilimin addini, daga ciki har da garin Hadejia, sannan ya tafi Maska, kana ya zauna Zaria daga bisani kuma Kano.

 

Shehu Adamu ya zama zaƙaƙuri acikin ilimi daban-daban, daga ciki har da ilimin li’irabi, wanda saboda kwarewar tasa ne ma ya ake masa inkiya da “Mai Li’irabi”.

 

Shekh Adam ya zauna a gidan Shehu Malam Tijjani ‘Yar mota, kuma yayi Tarbiyatul Azkar a wurin Shehul Hadi. Shehi ya zauna garin Chota ta ƙasar Niger don karantarwa ga daliban Shehun Chota, daga baya Shehu ya dawo Kontagora yaci gaba da yaɗa addini da kuma bada ilimi har sunan sa ya koma Shehu Adamu Kontagora,

 

Shehu Adamu Kontagora ya tsaya ka’in da na’in wurin hidima ga addinin musulnci da darika da kuma faila gaba daya, da ƙarfin sa da aljihun sa, Kamar dai yanda muka gani, kuma muka sani, aikin da ya gada a gidan su kenan.

 

Kuma har ila yau shima gidan sa na daya daga cikin manyan gidajen da ake bada ilimi a cikin garin Kontagora, da sauran ƙauyuka da ake kai wa karatun, kamar yadda aka saba tun yana raye.

 

Shehi yayi fama da jinya na rashin lafiya, kuma wannan bai hana shi bautar Ubangijin sa ba har ranar da yai wafati, an kai shi Minna da Nyamai a kasar Niger Republic dan neman lafiyar sa.

 

Shehu Adamu Kontagora yayi wafati a ranar wata Laraba da dare, 11/03/1424AH (Cikin watan Mauludil), Wanda yayi daidai da 13/05/2003AD, aka yi Janazar sa a ranar alhamis 14/05/2003AD, aka birne shi a Zawiyyar sa/gidan sa

 

Allah ya kara karamar Barzahu Alfarman Shugaba ANNABI Muhammadu ﷺ

 

Allah kabamu Albarkansa Dan Hidimar sa da Himmar sa. Amiiiin Yaa ALLAH

 

Safwan Jajjaye Rijau

Hadarar Shehu Habibu Garamu

Share

Back to top button