Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Biyar 5.

CIKAMAKIN WALIYAI (5)

 

TASOWAR SA DA NEMAN ILIMIN SA

 

Ko ban faɗa ba, mai karatu zai gane cewa duk wanda Allah ya azurta da irin wayannan iyaye, dole ya samu cikakken kulawa na ilimi da tarbiya, haka ne ya kasance ga Shehu Tijjani kuwa, domin bayan ya tasa kaɗan, sai iyayen sa suka mika shi gun babban waliyyi mai suna Sayyidi Abi-Abdallah Muhammad ɗan Hamu Almadawiy (ya rasu 1162H) domin yayi karatu, kuma cikin ikon Allah ya haddace Alqur’ani bisa ruwayar warshu a hannun sa yana da shekaru bakwai a duniya.

 

Wannan malamin na Shehu Tijjani, ya sadaukar da lokacin sa wurin ilimantar da yara da manya, kuma ya gaji haka ne daga wurin malamin sa wanda yake babban waliyyi mai suna Sheikh Isa Bu’akaz Almadawi RTA wanda ya ga Allah (SWT) a mafarki (ru’uya), ya karantawa Allah Alqur’ani mai girma a ruwayar warshu, Allah yace “masa tabbas haka aka saukar da shi, babu abinda ka rage ko ka ƙara”.

 

Allahu Akbar!

 

Shehu Ahmad Tijjani ya karanta littattafan fiƙihu da na furu’a da adab da sauran su tun daga kan su Ahalari, Ishmawiy, Risala, Ibn Rushid da sauran su a wurin babban waliyyi masanin Allah mai suna Sidi Mubarak Bu’afiya Almadawiy RTA.

 

Watarana Shehu Ahmad Tijjani RTA ya fito daga aji sai yaga haske daga ƙasa zuwa samaniya, sai Annabi SAW ya bayyana, yace masa “Cigaba da juriya, kana kan tafarki madaidaiciya “, Shehu Tijjani ya tsorata matuƙa, ya ruga wurin gwaggon sa mai suna “Jurkhum” ya faɗa mata sai ta kwantar mai da hankali ta bashi abincin da yake so. Shehu Tijjani yana son Jurkhum sosai kuma daga baya ya faɗi cewa waliyiya ce babba wacce babu abinda mutum zai tsaya kan kabarin ta ya roki Allah shi, na sharri ko alheri, face sai Allah ya amsa masa, dalilin haka aka daina nuna kabarin nata har ya bace.

 

Kafin Shehu Ahmadu Tijjani RTA ya cika shekaru ashirin da daya a duniya, ya gama da duk wani ilimi na littafi na ilimin Shari’a da Sufanci. Ilimin Shehu Tijjani da yadda yake saurin fahimtar abubuwa da haddace su, kyauta ce daga Allah, babu tamkar sa a cikin abokan karatun sa, babu wani abu da zai sa a gaba bai cimma karshen sa ba, ba shi da karaya ko tsoro ko fargaba ko kaɗan, duk da shekarun sa kadan ne, amma ya tara ilimi na ban mamaki kuma tuni labarin ilimin ya sa mamaye garuruwan dake kusa da Ainu Madhi har ma akan zo gareshi domin neman ƙarin bayani da fatawa.

 

ALLAH KA AZURTA MU DA ILIMI MAI AMFANI IRIN NA SHEHU TIJJANI, KAYI MANA TSARI DA ILIMI MARA AMFANI WANDA YAKE SA A ZAGI SHEHU TIJJANI RTA.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button