Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Daya (1)

CIKAMAKIN WALIYAI (1)

*

GABATARWA

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ce “Lallai waliyan Allah babu tsoro a garesu kuma ba zasu kasance suna yin baƙin ciki ba” (Suratu Yunus: 62). Dubun Salati da Aminci su cigaba da tabbata ga farkon halitta, cikamakin Annabawa kuma shugaban manzanni, wanda yake cewa “Allah yace duk wanda ya nuna kiyayya ga waliyyi na, hakika yayi shirin yaƙi dani” (Riyadus salihin: 95), A salatin kasa da iyalin sa da sahabban sa da bayin ka salihai.

 

Hakika nayi nufin hidima ga Shehu Ahmadu Tijjani RTA amma na rasa ta yadda zan aiwatar da haka, cikin falalar Allah sai naga dacewar in tsakuro tarihin sa daga taskar magabata domin in faranta ran masoyan sa dashi.

 

Ina mai neman uzuri da afuwa akan duk wani kuskure da mai karatu zai ci karo dashi cikin rubutun nan, ya karɓa da hakuri, ni bawa ne mai tsananin rauni.

 

1. HAIHUWAR SA

Maulanmu Shehu Ibrahim Niasse RTA yana cewa:

مولد الختم عام نقش تجلى * سيدا طاهرا وهو ذكاء

“Haihuwar cikamaki (na waliyai) ya kasance a cikin shekarar NAQ-SHIN, ya bayyana a matsayin shugaba mai tsarki mai cikakken hankali”.

 

NAQ-SHIN (نقش) shine 1150 a ilimin hisabi, wato harafin NUN yana daukar 50, QAF yana daukar 100, SHINUN yana daukar 1000. Abin nufi a shekara na dubu daya da dari da hamsin bayan hijirar Annabi SAW aka haifi Shehu Ahmadu Tijjani RTA, ranar 13 ga watan safar.

 

A garin “Ainu Madi” wanda yake kusa da laghouat a ƙasar algeria aka haife Shehu Ahmadu Tijjani RTA. Wannan garin yayi ƙaurin suna saboda tarin waliyan dake cikin sa tsawon zamani, kamar yadda Sidi Abdullahi ɗan Muhammad Al-iyyashi (wanda ya rasu hijira tana 1090) ya ruwaito a littafin sa mai suna “Rihila” bayan ya ratsa ta cikin garin a lokacin tafiye-tafiyen sa. Sidi Abdullahi ya sadu da kakan Shehu Tijjani kuma takwaran sa wato Sidi Ahmad, ya bayyana shi (Sidi Ahmad) a matsayin babban waliyi mai tarin ilimi.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button