Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Shida 6.

CIKAMAKIN WALIYAI (6)

 

AUREN SA DA RASUWAR IYAYEN SA.

 

Mahaifin Shehu Tijjani ya nema masa auren mace yar mutanen kirki mai cikakken tarbiyya a lokacin da ya zama matashi (ya balaga) domin ya tsare masa mutuncin sa da kuma samun rinjaye akan sharrin shaiɗan. A gidan mahaifinsa ya zauna da matar tasa cike da soyayya da begen juna. Kwatsam watarana a cikin shekarar 1166, a lokacin Shehu Tijjani yana da shekaru goma sha shida da haihuwa, cutar annoba ta kama mahaifi da mahaifiyar sa suka rasu tare, ance yini daya ne tsakanin su, Allah ya jaddada musu rahmah, Amin.

 

Shehu Ibrahim Niasse RTA yana cewa:

طَلَّقَ الشَّـيْخُ زَوْجَهُ إِذْ رَآهــَا * وَافَـقَـتْـهُ فِـي جِـدِّهِ الغَـيْدَاءُ

Shehu Tijjani ya saki matar sa a lokacin da ya ga kyanta na gogayya da himmar sa.

 

Wato Shehu Tijjani RTA yana zaune da matar sa lafiya lau amma sai ya ga akwai alamun himmar sa zata tawaya saboda dole ya raba lokacin sa na ibada da karantarwa ya ba matar tasa, bugu da ƙari can cikin zuciyar sa bashi da burin da ya wuce yayi tafiye-tafiye cikin duniya domin saduwa da manyan waliyai saboda ya riski abinda yake da buri na sha’anin yardar Allah.

 

Don haka watarana sai ya kira matar tasa ya nemi iznin ta akan ta yarda ya sauwaƙe mata (ya sake ta) saboda burin sa ba zai bashi damar sauke mata hakkokin ta na aure ba tunda tafiye-tafiye zai yi. Da yake mace ce mai albarka da fahimta saboda tarbiyar da ta samu, sai ta yarda kuma ta karɓi uzurin sa, ya bata dukiya mai yawa a matsayin kyautatawa gareta sannan ya sake ta saki daya kuma har zuwa lokacin rabuwar su, basu haihu ba.

 

Tarihi ya tabbatar sanadin wannan dukiyar ne matar da zuri’ar ta suka shahara fagen arziki saboda yawan sa da kuma albarkar Shehu Tijjani RTA.

 

✍️ Sidi Sadauki

Back to top button