Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA (Cikamakin Waliyai) Kashi Na Uku 3

CIKAMAKIN WALIYAI (3)

 

ƘABILAR SA (RTA)

 

Shehu Ahmad Tijjani RTA sunan ƙabilar sa “Abdah” (عبدة). Bisa al’ada, mafi yawan sharifai wayanda kakannin su suka yi hijira daga Madinah, sukan samu canjin ƙabila saboda auratayya a wata ƙasar, amma Shehu Ahmad Tijjani tasa ƙabilar bata sauya daga larabci zuwa wata ba.

 

Ƙabilar Abdah babbar ƙabila ce a ƙasar Morocco, sun zauna a ƙasar tun zamanin khalifancin muwahidin (خلافة الموحدين). Asalin su kuwa zuri’ar “Banu Ma’aƙil” ne wayanda suka yi hijira zuwa Morocco tareda kabilar “Banu Hilal” da “Banu Sulaym” a ƙarni na 11.

 

Jami’in diplomasiyya na ƙarni 19 ɗan ƙasar faransa mai suna “Eugène Aubin” yace ƙabilar Abdah suna da matukar ƙarfi, suna da kimanin ƙarfin makamai dubu talatin da biyar, kuma larabawa ne zalla, sun mamaye yanki mai albarka a ƙasar morocco, suna da arzikin dawakai da raƙuma kuma suna sahun ƙabilu biyar na “Quasi-Makhzen” a Morocco.

 

SUNAN SA NA “TIJJANI”

Daga Morocco ne Sayyidi Muhammad Salim (Na biyu) yayi hijirah zuwa Ainu Madhi na ƙasar Algeria.

 

Wannan kakan na Shehu Tijjani wato Sayyidi Muhammad Salim, Babban waliyi ne wanda ya riski mukamai 72 na ilimin Muhammadiya. Yana da ɗaki nasa shi kadai da yake shiga domin yin “halwa” da zikirori. Girman wulayar sa ta kai baya barin fuskar sa a buɗe a duk lokacin da zai fita daga gida zuwa masallaci, saboda duk wanda ya hada ido dashi, zai kamu da tsananin kaunar sa har yayi fiye da abinda mata suka yi na yanke hannayen su yayin da Annabi Yusuf ya gitta ta gaban su.

 

A Ainu Madhi din ne ya auri yar ƙabilar “banu Tujin/Tijan/Tijanata” wayanda suke karkashin ƙabilar “Berber” ko kuma “Amazig/أمازيغ”. Al’adar wannan ƙabilar, ya’ya suna dangantuwa ne da ƙabilar iyayen su mata, wannan ne yasa ake kira ko yin laƙabi ga ya’yan Sayyidi Muhammad Salim da “Tijjaniy”.

 

ALLAH SABODA SAYYADI MUHAMMAD SALIM, KA BIYA MANA BUKATUN MU DA GAGGAWA.

 

✍️ Sidi Sadauki

Back to top button