TARIHIN SAYYADA FATIMAH MATAR ALIYU BIN ALI DALIB (RA) Kashi Na Hudu (4).

JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

 

6⃣ MATSAYINTA A GURIN ALLAH(S.W.T) DA MANZON ALLAH(S.A.W):

 

Lallai Haƙiƙa NANA FATIMA(A.S) Tana Da Matsayi Mai Girma a Gurin ALLAH Da MANZONSA.

 

Mun Sani Ku San Komai Nata Sauƙaƙƙe Ne Daga Wajen ALLAH Maɗaukakin Sarki:

 

Sunan Ta Sauƙaƙƙe Ne Daga Sama, ALLAH Ta’ala Ne Yayo Wahayi Ta Hanyar MALA’IKA JIBRIL Cewa; A Samata Wannan Suna ‘FAƊIMA’.

 

Haka Nan Al’amarin Ɗaurin Aurenta, ALLAH Ne Ya Aiko Da Umarni Ga MANZONSA Cewa; Ya Aurar Da Ita Ga SAYYIDINA ALI(Karramallahu Wajhahu),

 

Shi Yasa Lokacin Da Wasu Daga Cikin Sahabbai Da Suka Nemi Aurenta Basu Samu Ba, Suka Ce Ma MANZON ALLAH(S.A.W) Mun Nemi Auren ‘FAƊIMA’ Baka Bamu Ba, Amma Ka Aura Ma ALIYU???

 

Sai Ya Ce Masu; Bani Na Hana Ku Ba ALLAH Ne Ya Hana Ku, Ya Aura Masa Ita, Haka Ma Lokacin Ɗaurin Auren Sai Da Aka Yi a Sama Gabanin Ayi Shi a Ƙasa Kai Hatta Likkafaninta Daga Gidan Aljanna Aka Zo Da Shi.

 

Haka Nan Ya Zo a Hadisi Daga MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce;

 

“Duk Wanda ‘Faɗima’ Ta Yarda Da Shi, To ALLAH Ya Yarda Da Shi, Wanda Kuma Take Fushi Da Shi, To ALLAH Yana Fushi Da Shi.”

 

Wato Dai ALLAH Yana Fushi Da Fushinta, Yana Kuma Yarda Da Yardarta.

 

A Wani Hadisi Kuma MANZON ALLAH Yana Cewa; “Azaba Ta Tabbata Ga Duk Wanda Ya Zalunce Ta Ko Ya Zalunci Zuriyarta”.

 

Daga: Imam Anas

 

ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA(A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

 

Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button