TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ ANNABI (SAW) Kashi Na Daya (1).

JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

 

An Haifi NANA FATIMA(A.S) Ranar JUMU’AH 20 Ga Watan JUMADA THANI a MAKKAH, A Shekara Ta Biyar Bayan Aiko MANZON ALLAH(S.A.W) a Shekarar Da Ƙuraishawa Suka Sabunta Ginin Ka’aba 605 AD.

 

1⃣ NASABARTA DA GIRMANTA A TAKAICE;

 

Nasabarta Ta Wajen Mahaifinta, NANA FATIMA;

 

Ƴar MUHAMMADUR-RASULULLAHI,

Ɗan Abdullahi,

Ɗan Abdul-Muɗallib

‘Ɗan Hashim

Ɗan Abdul-Munafi

Ɗan Kusayyi

Ɗan Kilabin

Ɗan Murarata,

 

Ta Zarce Har Kan Adnan, Daga Nan Kuma Har Zuwa Kan ANNABI IBRAHIM(A.S).

 

Nasabarta Ta Wajen Mahaifiya NANA FATIMA(A.S) Ƴar NANA KHADIJA(R.A) Ce,

 

Ƴar Khuwailadin

Ɗan Asadin

Ɗan Abdul-Uzza

Ɗan Kusaiyin

Ɗan Kilabin

Ɗan Marrata,

 

Nasabar MANZON ALLAH(S.A.W) Ta Haɗu Da Ta NANA KHADIJA(R.A) Tun Akan Kakansa Na Huɗu Wato Kusaiyi.

 

Nasabar NANA FATIMA(A.S) Kenan a Taƙaice.

 

Malamai Sun Tafi Akan Cewa; Dukkan Ƴa’yan MANZON ALLAH(S.A.W) An Haife Sune, Kafin Zuwan Annabta,

 

Sai Dai Ita Kaɗai Aka Haifa Bayan Aiko SHI(S.A.W) Tare Da Ɗan-uwanta Ibrahim Ɗan Mariyatul Kibdiyya,

 

Shi An Haife Shi a MADINA Bayan Hijira Da Shekara Takwas Ya Rayu Kwana Saba’in Dai Dai.

 

2⃣ RAYUWARTA;

 

Haƙiƙa NANA FATIMA(A.S) Ta Rayu a Gidan Annabci, Kuma An Tarbiyyance Ta a Gidan Annabta, Tana Da Shekara Biyar Mahaifiyarta Ta Yi Wafati,

 

Tana Da Shekara Takwas Lokacin Da Aka Yi Hijira Zuwa MADINA, Bayan Komawa MADINA Anan Ta Rayu Shekaru 18 a Wata Ruwaya Shekaru 23 Ne, Ta Haifi Ƴaƴanta Guda Biyar, Maza Uku, Mata Biyu.

 

1. HASSAN.

2. HUSSAIN.

3. MUHSIN.

4. ZAINAB.

5. UMMU KHUL-SUM.

 

Daga: Imam Anas

 

ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA(A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

 

Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

Back to top button