TARIHIN SAYYADA FATIMAH YAR’ MANZON ALLAH (SAW) Kashi Na Biyar (5).

JIMADA THANI Watan Haihuwar Tsokar Jikin MA’AIKI(S.A.W); NANA FATIMA AZ-ZAHRA’U

 

7⃣ FALALAR SON SAYYIDA FATIMA(A.S);

 

Aƙwai Hadisai Masu Yawa Da Aka Ruwaito Daga MANZON ALLAH(S.A.W) Akan Falalar Son SAYYIDA FATIMA(A.S);

 

1. MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Ce;

 

“Duk Wanda Ya So Faɗima Ƴa Ta, To Zai Kasance Cikin Aljanna Tare Da Ni.”

 

2. A Wani Hadisi Kuma MANZON ALLAH (S.A.W) Ya Ce, “Son Faɗima Yana Amfanar Mutum a Wajaje Ɗari Daga Cikin Wajajen Akwai Lokacin Mutuwarsa, Zamansa a Ƙabari, Ranar Ƙiyama, Kan Siraɗi Da Kuma Wajen Hisabi.

 

A Wata Ruwaye Ya Zo Akan Cewa; Son Faɗima Alama Ce Ta Imani, Ƙinta Kuma Alama Ce Ta Munafurci.

 

A Wata Ruwaya Kuma MANZON ALLAH Ya Ce; “An Sanya Ma Faɗima Suna Faɗima Ne Domin ALLAH Ta’ala Ya Yaye Duk Mai Sonta Daga Wuta.” – Wato Ma’ana Bashi Ba Wuta.

 

8⃣ WAFATINTA;

 

Akwai Ruwayoyi Kusan Goma Da Suka Yi Magana, Amma Ruwayar Da Tafi Shahara Wacce Ni Nafi Gamsuwa Da Ita, Kuma Na Gani a Littaffan Manyan Magabata Ita Ce Uku Ga Watan Jimada Thani Shekara Ta 11 Bayan Hijira.

 

9⃣ KABARINTA;

 

Shima Wannan Akwai Saɓani Na Ainihin Inda Kabarinta Yake Amma Akwai Zantuka Uku Wasu Sun Ce a Baƙi’a Yake, Wasu Sun Ce Yana Tsakanin Kabarin MANZON ALLAH (S.A.W) Da Minbarinsa, Wasu Sun Ce Yana Cikin Ɗakinta.

 

Allahu A’alam.

 

Jama’a NANA FATIMA (A.S) Tana Da Girma Da Martabar Da Bazamu Iya Faɗar Taba Sanin Haƙiƙanin Girmanta Da Martabarta Da Darajarta Sai Mahaliccinta.

 

Assalatu Was-Salamu Alaiki Ya Ummul-Mu’uminin

 

Daga: Imam Anas

 

ALLAH Ka Sanya Mu Cikin Jerin MASOYA NANA FATIMA (A.S), Ya Ƙara Mana ƘaunarTA (A.S)

 

Amincin ALLAH Ya Ƙara Tabbata Ga CIKAMAKIN ANNABAWA DA MANZANNI (S.A.W). Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button