TARIHIN SAYYADINA ALI ƊAN ABU ƊALIB (RALIYALLAHU ANHU) KASHI NA DAYA (1).

TARIHIN SAYYADINA ALI ƊAN ABU ƊALIB RALIYALLAHU ANHU DAGA TASKAR UMAR CHOBBE

 

Ali ɗan Abu Ɗalib Raliyallahu Anhu Sunansa da Asalinsa

 

Sunansa Ali ɗan Abu Ɗalib ɗan Abdul Muɗɗalib ɗan Hashim.

 

Shine ƙanin Manzon Allah, domin kakansu ɗaya shine, Abdul Muɗɗalib.

 

Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima ɗiyar Asad ɗan Hashim wadda ita ma ta gama kaka da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

 

TASHINSA/GIRMAN SA

An haifi Sayyadi Ali a shekara ta ashirin da uku kafin Hijira, an aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin Ali yana da shekara goma.

 

ANNABI S.A.W ya girmi Ali da shekaru talatin. Kuma kamar yadda mahaifinsa ya riƙa Manzon Allah ya kula da shi, shi ma Manzon Allah ya riƙa Ali ya kula da shi.

 

Darajojinsa kasancewar Sayyadi Ali ya tashi a hannun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tun ba a aiko shi ba, ya bai wa Ali damar ya shaƙi ƙamshin Musulunci tun a rana ta farko.

 

Sayyadi Ali kuwa bai yi wata wata ba ya amsa kiran Allah a hannun yayansa kuma mai gidansa.

 

Don haka Sayyadi Ali shine mutum na farko da ya karɓi addinin Musulunci bayan matar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Nana khadijah.

 

Duk da kasancewarsa yaro ne ƙarami, amma Ali ya ba da gudunmawa wajen kafuwar Musulunci. A tare da shi aka yi Bai’atul Aƙaba, wadda Allah yace, ya yarda da waɗanda su kayi ta.

 

Haka kuma ya kwanta a kan shimfiɗan ANNABI S.A.W a lokacin da zai yi hijira.

 

A yaƙin farko da aka yi tsakanin Musulmi da Mushrikai, yaƙin Badar, Ali ya yi fito na fito da babban arnen nan Walid ɗan Utbah kuma ya kashe shi.

 

Sannan ya taimaka ma baffansa Hamza wajen kashe mahaifin wancan na farkon, Utbah ɗan Rabi’ah.

 

A yaƙin khandaƙ kuma shi ya yi fito na fito da Amru ɗan wuddu al Amiri wanda jarumawa ke fargaban karawa da shi, kuma Ali ya halaka shi.

 

A ranar yaƙin Khaibar kuma shi aka baiwa tuta bayan da ANNABI S.A.W yayi alƙawarin bayar da ita ga wanda ya siffanta da cewa, yana son Allah da Manzo kuma Allah da Manzo na sonsa.

 

Sayyadi Ali ya auri ‘yar Manzon Allah, Fatimah, wadda bai yi ma ta kishiya ba har Allah ya karɓi rayuwarta.

 

Sayyadi Ali shine ya zamo gwamnan Madina a lokacin da Manzon Allah ya fita da mafi yawan Sahabbai zuwa yaƙin Tabuka.

 

Wannan ya sanya Ali bai ji daɗi ba don rashin kasancewa tare da ANNABI S.A.W da manyan Sahabbai.

 

Amma ANNABI S.A.W ya kwantar da hankalinsa da cewa, matsayinsa a wurin Manzo yayi daidai da na Annabi Haruna ga yayansa Musa, duk da yake shi ANNABI S.A.W ba wani Annabi a bayansa.

 

Allah ya bamu Albarkacin dukkan Sahabban ANNABI S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button