Tarihin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Kashi Na Hudu (4).

MAI TAMBARIN ZIKIRI DATTIJO MAI ABUN MAMAKI MAULANA SHEIKH ALIYU HARAZIMI HAUSAWA (RADIYALLAHU ANHU) (IV) Hudu 4.

 

Har yanzu muna cikin goman farko ta watan Zul Hajji wanda a cikin irin kwanakin Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa (Radiyallahu anhu) Ya kasance a wannan duniya. A ranar 9 ga wata wanda a ranar ake tsayiwur Arfa..

 

Insha Allahu zan ɗora da tarihin ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa (Radiyallahu anhu) Na tsaya a inda na ke bada tarihin zaman Maulana a wajen shahararren waliyin nan Sheikh Muhammadu Gibrima (Radiyallahu anhu).

 

Shehu ya dawo garin Kano da zama bayan wafatin Shehinsa Muhammadu Gibrima (Radiyallahu anhu) wanda yayi wafati a shekarar 1975 duda akwai maganganu da suke tabbatar da cewa dama yana zaune a cikin birnin Kano tun kafin wafatin Shehinsa.

 

Shehu ya cigaba zama a zawiya da ke unguwar Hausawa da ya gada a wurin mahaifinsa, Shehu ya kwashe sama da shekaru sittin na rayuwarsa yana karantarwa, da horar da zuciyar Bayin Allah ta koma tsarkakiya da kaddamar da dimbin almajirai a Kano da wajenta.

 

Littattafai da yawa Shehu ya rubuta, wasu an buga su, wasu kuma suna yawo a matsayin rubuce-rubuce a tsakanin mu mu mabiyansa. Amman a matsayinsa na Sufi wanda babban abin da ya dame shi shi ne koyar da mai son samun Allah a sauƙaƙe yadda ake tsarkake zuciya Nafs al-Ammara (ƙananan ruhi) don ya mayar da ita cikin Nafs al-kamila cikakken samun zauƙin Ubangiji.

 

Maulana Shehu Aliyu Harazimi (Radiyallahu anhu) Ya rubuta littattafai da dama a fagen ilimin halin ruhi. Waɗanda sun haɗa da, wani littafi mai suna , Kasr al-nufus da kuma wani littafi mai suna Juhud al-‘ajiz (‘Ƙoƙarin marasa ƙarfi’).

 

Waɗannan littattafai sun tattauna akan matakai daban-daban da ƙalubalen da mai neman Allah yake zai fuskanta yayin ƙoƙarinsa na samun wusuli.

 

Wani fanni da Shehu kuma ya yi rubuta a cikinsa shi ne nau’inkan Salati ga Annabi (Sallallahu alaihi Wa sallama) . Ba sai na yi bayanin yanda muhimmancin salati ga Annabi a wajen Muslimi musamman Sufaye. Domin daruruwan Sufaye da yawa, sun yi rubutu wanda suke tabbatar da shine ya zama ginshiƙin tafarkin ruhi, kamar yadda aka yi imani da cewa yana ba wa mai buri damar shiga ‘halarar Annabi’ (al-hadra al-Muhammadiyyah) kuma ya sami haske.

 

Wannan gaskiya ne musamman a cikin tafiyar Sufaye, wanda ya zama koyarwarmu mun yi imani cewa haƙiƙanin Annabi (al-Haqiqa al-Muhammadiyya) shine farkon halittar Allah kuma shi ne ruhin Duniya (al-Nafs al-kulli) ya mamaye wuri na tsakiya.

 

Wasu daga cikin manyan malaman Darikar Tijjaniyya.. sun rubuta littafai irin nasu na salati ga Annabi, wadanda ake karantawa a Najeriya a yau. Wasu misalan sun hada da;

Akwai littafi mai suna Yaqutat al-muhtaj, wanda Shehu Muhammadu al-Damrawi ya rubuta (wanda ya rasu a shekara ta 1799), wanda ya kasance aminin Shehu Ahmad al-Tijani (Radiyallahu anhu)

 

Akwai shahararren littafin nan na Salati mai suna Al-Tibb al-fa’ih, wanda Sheikh ‘Abd al-Wahid al-Nazifi ya rubuta wanda yayi wafati a shekarar 1948.

Da kuma litattafai da dama kamar irin wanda Shehun Najeriya Sheikh Muhammad Gibrima Shehin Maulana ya rubuta, wasu daga cikin litattafan Salati akwai.

 

Jihaz al-sarih…da

Nata’ij al-Safar.

 

Shima Sheikh Aliyu Harazimi Radiyallahu anhu ya tattara nasa salati ga Annabi sun hada da; Sullam al-muhibbin ila hadrat khayr al-mursalin Sannan akwai shahararren littafin nan mai suna Sir al-asrar (‘Sirrin Sirri’), duka an buga su a Kano.

 

~Mujaheed M Muh’d

Back to top button