TARIHIN WALIYAI: Takaitacce Tarihin Sheikh Ibrahim Modibbo Umar Jarkasa Kano

TAƘAITACCEN TARIHIN SHEHU IBRAHIM MODIBBO UMAR JARƘASA.

 

NASABARSA:

Sunanshi Ibrahim ɗan shehu umar wanda aka fi sani da (Modibbo Jarƙasa) ɗan umar ɗan umar wanda ya ƙauro daga maiduguri ya dawo jigawa ɗan yakubu ɗan abubakar (Albarnawi).

 

RAYUWARSA:

Shehu ya rayu rayuwa mai tarin albarka. An haifi shehu a garin kano unguwar kabara layin jarƙasa. An haifeshi ranar juma’a, yayi wafati ranar talata 16/08/2022. Shekarunshi sittin da uku da wata uku da kwanaki. Anyi jana’izarshi ranar da yayi wafati a gidansa dake sharaɗa layin shehu ibrahim jarƙasa cikin garin kano.

Shehu yayi wafati ya bar mata biyu da yaya goma sha biyu, maza 5 mata 7.

 

SUNAYEN ƳAƳANSHI:

1- Sayyadi Umar Halifa

2- sayyadi Muhammadul Habib (Habibu)

3- Shehu Ahmad tijjani (Abul abbas)

4- Sayyadi Mustapha

5- Sayyadi Muhammad Al’amin

1- Sayyada Ummi

2- Sayyada Mabruka

3- Sayyada Mubaraka

4- Sayyada Hajiya

5- Sayyada Humaira

6- Sayyada Zainab

7- sayyada Batulu

Shehu yana da jikoki guda huɗu daga ɓangaren ƴaƴanshi mata.

 

TAFIYE-TAFIYENSHI:

A tsawon rayuwarshi yaje hajji sau goma sha huɗu kamar yadda yake faɗa. Sannan yaje umra ba adadi, domin an taɓa tambayarsa sau nawa yaje umra yace shima bai san adadi ba amma yaje hajji sau goma sha huɗu. Yaje ƙasar misra sau uku. Yaje umra sau biyu a halin bashi da lafiya bayan ya dawo daga umrarshi ta ƙarshe ya kwanta a asibitin Malam Aminu Kano har tsawon sati biyu.

 

HALAYEN SHEHU:

Duk makusanta Shehu tun daga iyalai, malamansa, muridai da ƴan uwa sun shaida shi mutum ne mai hakuri, ladabi, tawari’u, tsoron Allah, gudun duniya, tsantseni, tausayi, jinƙai da kuma bin shari’a da haƙiƙa. A lamari na bin shari’a tunda ya fara rashin lafiya bai taɓa fashin zuwa sallar jumma’a ba sai dai idan yana asibiti, domin ko lokacin da jikinshi yayi tsanani ana kaishi masallaci. Sannan bai taɓa fashin sallah a jam’i ba, da sauran ababe wanda ni ban isa na furtasu gaba ɗaya ba.

Shehu yayi jinya na tsawon shekara huɗu da wata huɗu, ya rasu ranar 16/08/2022.

 

Wannan taƙaitaccen tarihin Shehu Ibrahim Modibbo Jarƙasa kenan.

 

Allah ya bamu albarkacinsa saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Amiin

 

Mustapha Abubakar Kwaro

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button