Takaitacce Tarihin Sheikh Imam Mansur Kaduna.

Murnar Ƙarin Shekera Sheikh Ibrahim Mansur Imam Kaduna Rta.

 

Tattaunawa ta musamman da Sheikh Ibrahim Mansur Imam Kaduna.

 

Sheikh Ibrahim Mansoor Malami ne matashi kuma mabiyin ɗariƙar Tijjaniya, amma kuma wanda a kullum fatansa shine a haɗa kai a zauna lafiya tsakanin dukkan Musulmi ko kuwa masu bambancin aƙida ne, inda Sheikh Mansoor ya kasance bai yarda da rarrabuwa ba, don aƙida. Ga dai yadda Wakiliyar Blueprint Manhaja, BILKISU YUSUF ALI, ta gana da shi:

 

Za mu so mu ji taƙaitaccen tarihinka

 

Sunana Ibrahim amma mahaifina yana kirana Inyas kakana yana kira na Barhama ‘yan’uwana suna kirana Shehu. Sunan mahaifina malam Mansur. An haifeni a cikin garin Kaduna a wata unguwa da ake kirantaTudun Nufawa sunan mahaifiyata Hajiya Aisha mu bakwai ne a wurin iyayena. Na fara karatun Al’ƙur’ani a wata makaranta Nurul Islam wadda ake kira Madinatul Ahabab talamiz yanzu. Na yi saukar Alƙur’ani a 1986 sai mahaifina ya ce na yi ƙarami sai a bari a 1987 aka yi bikin aka yanka min rago kamar yadda aka saba a ƙasar Hausa an yi wannan ne bayan wafatin mahaifina wanda kullum yana zaburar da ni da in na yi saukar Alƙur’ani zai kai ni madinatu kaulak.

 

Babana shi ne malamina na farko shi ya kowa min karatu musamman gajerun surori shi ya koyar da ni salatul fatih da jauharatul kamal. Malamai na a lokacin bayan mahaifina akwai malam Muhammad Hashim. A 1990 sai aka buɗe makarantar haddar Alƙur’ani anan makarantarmu na shiga muka kammala hadda a 1992. Babban malamina a cikinsu shi ne malam Mukhtar Ibrahim da malam Ahmadi akwai malam Habib limamin Barkum da malam Ridwan shugaban makarantar fityanul islam Kaduna. Na yi makarantar firamare a wata makaranta da ake kira sunusu 1 1882 -1986 na yi sakandire na yi makaranta conferehensive sannan na yi smc na yi. Na yi karatu a wurin malam Abdulkarim Hashim limami ne yanzu a Kaduna da sayyadi sheikh malam Ibrahim Shehi da malam Rufa’i har yanzu kuma ana karatun ba a tsaya ba.

 

Ya maganar Ɗariƙar Tijjaniya?

 

Marji’ina gaba ɗaya na ɗariƙa shi ne maulana sheikh Abulfathi kuma har yanzu ni almajiri ne kuma har yanzu ni maridi ne don haka duk inda na ga maridai ina kallonsu a matsayin ‘yan’uwana duk inda na ga shaihunnai da muƙaddimai ina kallonsu a matsayin shaihunnai na kuma shuwagabannina ni duk wani da yake cewa shi almajirina ne ko muridi ni ina kallonsa ne a matsayin aboki.

 

A baya ka yi maganar Kaulaha an je can da karatun?

 

A’a ban je Kaulaha da neman karatu ba amma na je don neman madadi don haka nakan je lokaci zuwa lokaci musamman lokacin mauludi haka duk wuraren da a ke faɗa a cikin diwani wanda ya shafi Shehu na je misali Sham da Kosi Ɗaiba da Kaulak.

 

Ka yi majalisai da dama kan littafin diwani na shehi Ibrahim me diwani ya ƙunsa?

 

Shi diwani yana magana ne akan Annabi Muhammad(S.AW) gaba ki ɗayansa yana magana ne kan siffofinsa da halayensa da ɗabi’unsa wani lokacin za ka ji Shehu Ibrahim yana faɗar ayyuka irin na annabi da ainihin tsagwaron kyau na Annabi da yadda yake siffanta Annabi da ilimi da kyauta da baiwa da taka-tsantsan wurin kada saɓi Allah duk da shi Annabi ba ya ko ɗarsa saɓon Allah a zuciyarsa. Don haka in ana son a koya wa mutum tsantsar ƙaunar Annabi to a koya masa diwani.

 

Ya ka ke ganin ɗariƙar Tijjaniya a halin yanzu da bambanci a lokutan baya?

 

Ɗariƙar Tijjaniya tana nan yadda take sai dai a ce ‘ya’yan cikinta in har an ga wani abu saɓanin shari’a ko hankali amma ɗariƙa ginin Allah ne saboda gini ne da aka gina shi da abubuwa guda shida ginin ɗariƙa an yi foundation me kyau shehunnanmu suna cewa an gina harsashin gininmu na ɗariƙa da abubuwa guda shida Alƙur’ani da hadisi (sunna) duk kuwa ginin da aka yi da Ƙur’ani da sunna ba zai rusu ba sannan kuma masu ginin ba sa ginin da haramun sai sun ci halal sannan ba sa yin ginin da rashin tsarki kamar janaba ko ƙazanta da tsarki suke ginin kuma ana yi ana zikiri kin ga wannan ginin yana da ƙarfi don sun nisanci saɓon Allah sune maginan ga yawan tuba ana ginin ana tuba istigfari ba yadda za a yi a cikin maginan a samu wani ya tauyewa matarsa ko yayansa ko iyayensa haƙƙinsu ko dangi ko makwabta sai wanda ya ba wa duk mai haƙƙi haƙƙinsa saboda haka yanzu wannan ginin da bayin Allah suka yi wa zai iya rusa shi. Abubuwa da yawa da ake yi ba yan ɗariƙa ba ne suke yi kaidi ne da makirci amma ba kowa ba ne ya san hakan.

 

Kaidi ne da makirci wanda bai da ido bai da kwalli ba zai gane ba.Zai ga an yi waƙa an zagi Allah ko ka ga wasu samari sun yi gungu su ce su ba za su yi sallah ba, sai a ɗauka wannan yana cikin ɗariƙa wanda suke magana da sunan haƙiƙa wanda haƙiƙar nan shi ne ilimi na ƙarshe, waɗanda ba su san abin in an kai musu irin wannan ƙorafin sai su ɗau lasifika su yi ta ɓaɓatu suna surutai a kan abin da maƙiya Allah suka shirya. Da za a ce su faɗi shehinsu za a tarar ba su da shi. Irinsu kuma su suke samun yara ƙanana marasa ilimi su yaudare su su kuma irin waɗanda ake yaudarar tasu ba su da shehunnai sai su fake da wani Shaihu mai gaskiya har yake yayatawa shi Almajiransa ne kuma da za a je wurin Shehun bai ma san shi ba. Irin waɗannan in ba ba don an gina ɗariƙar da waɗannan manyan duwatsun ba da waɗannan matsalolin sun isa su rusa ɗariƙa.

 

Lazimi da wazifa da zikirin juma’a su ne ɗariƙa ina son duk wanda ya karanta wannan yake lura da duk wanda yake magaba akan ɗariƙa ko Shehu Tijjani ko Shehi Ibrahim wata rana ka je ka ziyarce shi ka yi kwana uku ka ga in an idar da sallar asuba yana lazimi haka da la’asar yana wazifa a cikin jam’i, za ka ga su ma su wa’azin daban ba ma ɗariƙar suke ba ba ma su da zawiyoyin ba su da muridan. Wasu almajirai gare su na ilimi, akwai kuma bambanci tsakanin almajirai masu neman madadi da almajirai masu neman ilimi. Akwai malaman Zawiya da da malaman Jami’a, dukansu babu abin wulaƙanta wa to amma kowa da aikinsa sai ka ga ana neman haɗa kindirmo da miya a rinƙa ba su fatawa su amsa. Wanda bai rayu a zawiyya ba bai san mene maridantaka ba bai san abubuwa irin na muridai ba bai san yadda ake suluki da intizali halwa da zikirori , duka bai yi wannan ba sai a ɗauko matsalolin zawiyya a ce ya amsa ko a ɗauki matsalar Jami’a a kai wamalamin da ke zawiyya ta ya ya zai fahimta? Ɗariƙa na nan sai dai mu ‘yan ɗariƙa ne ya kamata mu dawo mu duba shin abin da shehu Amadu Tijjani ya bar mu muna kai ko abin da Shehi Ibrahim ya koyar da mu muna kai ko kuwa mun sauya musu abin su da manufofin su?

 

Don wasu sun lalace a cikinta ba za a ce kowa ya lalace ba. Kamar Musulunci ne don an samu wasu sun yi laifi ko an kama wani da laifi ba za a yi wa kowa kuɗin goro ba. Misali an taɓa kama wani mai laifi aka tambaye shi shin ka san Allah? sai ya ce “ya za a yi na san shi, shi yana can ni ina nan?” Kuma Musulmi ne. Ire-iren wannan wanda bai san ɗariƙa ba sai ya yarda amma wanda yasan ɗariƙa yasan ƙarya ne.

 

Ya ka ke kallon haɗin kai da muhimmancinsa?

Haɗin kai a addini abu ne mai kyau babu abin da ya kai haɗin kai daɗi to amma abin da yasa haɗin kai yake da wuya shi ne saboda mayaudara sun shigo cikin al’amarin da maƙaryata masu neman girma da abinci da duniya da almajirai wanda su kuma in aka haɗa kai ƙaryarsu ta ƙare amma ai babu abin da yakai haɗin kai daɗi duk jama’ar da suka yi ƙarfi haɗin kai ne ya kawo musu duk jama’a in ta yi rauni rashin haɗin kai ne ya janyo mata. Misali a ɗariƙar Tijjaniya babu abin da babu, a cikinmu akwai ‘yan boko da Sarakaida Arifai da Malamai.

 

Kowa yana da ranarsa kowacce zawiyya akwai sirrin da shehu ya ajiye a cikinta kowanne muƙaddami akwai abin da Allah ya kevance shi don haka rarrabuwa shi ne babbar matsala. Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka munafikai da maqiya Allah ba su yi nasara akanmu ba. Yana da kyau ake zama ana tattaunawa muƙaddamai su haɗa kai ana jin koken juna da an gano waɗansu abubuwa akwai waɗanda su aikinsu haɗa husuma ne kawai. Ba kuma iya ‘yan ɗariƙa ba duk al’umma ya kamata su zauna lafiya su haɗa kai musamman Musulmi da Musulmi don ci gaban ƙasa.

 

Ya ɗan ɗariƙa ya kamata ya kalli wanda ba aƙidarsu ɗaya ba?

 

Shi ɗan ɗariƙa da masoyin ɗariƙa da ‘ya’yan ɗariƙa da ma agololi a ɗariƙa. Akwai waɗanda ɗariƙa ta haife su akwai waɗanda ɗariƙa ta riƙe su. Wato akwai bambanci tsakanin ɗan gida da ɗan riƙo a gida, ɗan gida ba zai taɓa tona asirin gidansu ba amma ɗan riƙo in aka ci karo da marar amana zai iya tona asirin komai na gida. Abin da ɗan ɗariƙa na gaskiya yake yi shi ne ya girmma duk halittar Allah tun daga kan dabbobi har ma kafirai da waɗanda ma ba addininsu ɗaya ba. Domin ɗan ɗariƙa na haƙiƙa in har yana da maƙwabci kirista ba zai iya kwana yana da abinci a gidansa ba ya bar maƙwabcinsa kiristan ya kwana da yunwa, saboda kiristan ɗan adam ne ɗan uwansa ko Musulunci bai haɗa su ba mutuntaka ta haɗa su . Misali idan aka ce kirsimeti ta yi aka ce wannan kiristan bai da abinci da ɗan bunsurun da zai yanka zai iya ba shi abincin da bunsurun amma ba zai ba shi kuɗin ba don kada ya sai alade, wannan zai sa ya ji daɗi har ma ya yi kwaɗayin addinin naka. Wannan shi ne asalin sufanci.

 

Shi yana kwaikwayon halayen Annabi Muhammadu (S.A.W) ne. In mutum yana ɗariƙa ba zai cuci kirista ba balle a dawo a ce ɗan izala ko shi’a. Wanda ya yi zurfi a ɗariƙa, zurfi na zikiri, zurfi na salati ga Annabi, zurfi na ma’arifa da tafakkuri da murafaƙar Allah shi zai iya gane wannan. Shehu bai koyar da aibata kowanne Musulmi ba kai hatta wanda ba addininmu guda ba misali, Sheh Ibrahim ya zo Kaduna, bayan shehu Ibrahim ya gama majalisi sai wani mutum ya ce masa “akrimukallahu ya kamata ka janyo hankalin mutane don kana da wani maƙiyi babba a garin nan ka ɗan yi magana sai Shehi Ibrahim ya katse shi ya ce “wa ne wannan maƙiyina?” da mutumin ya faɗi sunansa sai Shehu ya ɗago kai ya kalli wannan mutumin ya ce “ni b a ni da maƙiyi Musulmi idan kuma Musulm yana ƙina to na yafe masa”. Don haka ƙa’ida idan mutum yana cikin ɗariƙa ba a so ya shagaltu da wani yana qina wane ɗan izala ne ya zage shi, a yi zikiri kawai in kana da wadata ka taimake su ɗan izala ko ɗan shi’a ɗan’uwanka ne kada ka yarda wani abu marar dadi ya same su ka ji daɗi. Misali wani abu da ya faru da ‘yan shi’a aka ce wai Musulmi suna murna. Kada ka kuskura ka yi murna ka ce Allah ya jikan musulmi, zagin Sahabbai da ake cewa suna yi Allah ya shirye su, Allah ya sa su gane kuskure ne babba wanda zai iya fidda mutum daga addini in za a yi jana’iza in kana kusa ka je, in ka san wani nasu ka je ka yi musu taaziyya. Idan idonka yana da saurin hayawaye ka zubar da hawaye ya fi a ce ka yi murna.

 

Dan ɗariƙa so ake ya shagaltu da aikin Shehu Tijjani ya sa shi ba ya shagaltu da zagin ‘yan izala ba. Shehi Ibrahim yana cewa kada ku zagi kowa har abada kada ku doki kowa har abada, in kuma an zage ku ko an dake ku to ku yi haƙuri daman don haƙuri aka yi ku. Annabi SAW da ransa an an zage shi amma zagin bai cutar da shi ba. Haka bayan wafatinsa sahabbai an zage su ƙarewa har kisa to kai wa ye? Don an ce ma kafiri ko mishriki to kuma mene ne?

 

Waɗanne garuruwa ka ziyarta?

 

Na ziyarci Annabi har sau uku na yi hajji da umara na ziyarci Sayyada Faɗima (AS) na ziyarci ‘ya’yanta na ziyarci manyan sharifai jikokin Annabi, na je Aljeriya Ainamadi mahaifar shehi Ahmadu Tijjani, na je Maroko na ziyarci kabarin Shehu Tijjani a Fas na ziyarci jikansa a Kurdan na ziyarci Sayyadi Ahmad Ammar (wanda ake buga hotonsa ana cewa Shehu Tijjani ne) shi sun yi gwagwarmaya da Turawan Faransa sosai. Na je Senegal Madinatu Kaulak na je Ghana da Kamaru da Nijar da Barkina faso da dai sauransu. Kuma ziyara ce da duk na yi saboda Allah ba wai kasuwanci ba.

 

Kana sana’a ko kuma da wa’azi da koyarwa aka dogara?

 

Ina yin sana’a ni ban taɓa dogaro da wani ba na gode wa Allah, kuma ina gaya wa abokaina ‘yan Faila da Tijjaniya cewa ku dogara da kansu saboda in ka dogara da wani ko dai ya rasu ko ya gaji ko ya faɗi ko ya kore ka, to idan ɗan’adam ya gane wannan to sai ya dogara da Allah. Na kan ce dai su voye sana’ar kuma sana’a ya zama dole ka yi gaskiya.Ya kamata mutum ya zamana yana ajiye komai a matsayinsa idan karatu ya haɗa mu mu yi maganar karatu idan ɗariƙa ta haɗa mu mu yi idan ma’arifa ce faira mu yi maganar idan maganar aure ce in mun haɗu mu yi maganar. In ɗan’uwa ne ko maƙwabci kai hatta maƙiyi in an haɗu akwai irin maganar da ta dace a yi komai a ajiye shi a inda yake sauran sai ka bar wa Allah.

 

Wanne abu ne ke birge ka?

 

Ni ba a bin da yake birge ni a rayuwa kamar Shehu Ibrahim Nyass saboda duk abin da nake so yana cikinsa. Daga wurinsa na gani ni ina son Allah daga wurinsa na gani ina son Annabi Muhammad (SAW) kuma ni ban taɓa ganin masoyin Annabi kamarsa ba. Ina son Shehu Amadu Tijjani ban taɓa ganin masoyinsa kamar Shehu Ibrahim ba. Ina son waliyyai kuma su ne shaihannanmu to tarbiuyyar da ya ba su har muka ji muna sonsu shi ne ya ba su.

 

Me ka ke ganin zai gyara ƙasar nan?

 

Ni abin da nake hangowa a gyaran ƙasar nan saboda abin da za a gyara ƙasar nan shi ne a dawo kan koyi da abin da Annabi Muhammadu (S.AW) ya zo da shi. Ba wai ƙasar nan ba duka duniyar ma shi ne mafita. Ba musulmi ba Bature kafiri yana cewa “da za a zaunar da Annabi (S.AW) a kan kujera a kawo masa kofin shayi sannan a nuna masa duka matsalar da duniya take ciki to kafin ya shanye wannan kofin shayin sai ya warware komai”.

 

Don haka matsalar ƙasar nan an bar komai ne na koyarwarsa, shugabanni sun zama azzalimai miyagu su kuma mabiya sun zama ‘yan ta’adda ta ya ya ƙasa za ta gyaru? don haka in har ana son ƙasa ta gyaru sai an bi umarnin Annabi Muhammad (SAW) babba ya ji tausayin na qasa na ƙasa kuma ya yi biyayya.

 

Mene ne burinka?

 

Barina a duniya shi ne saduwa da manzon Allah(S.A.W) ina son na ji shi a komai nawa

 

Akwai Bambanci tsakanin Tijjaniya da Faira ne?

 

Babu wani bambanci abu guda ne faira da tijjaniya duk abu guda ne. Faira da ɗariƙa shi ne wannan zikirorin nan lazimi wazifa zikirin juma’a. Faira wani mataki ne a cikin ɗariƙa, faira shi ne sanin Allah ma’arifa saboda haka akwai ilimin shari’a akwai ilimin ɗariƙa akwai ilimin haƙiƙa amma masu ɓata abin sune za ki ji suna cewa ai haƙiƙa shi ne zina, ai haƙiƙa shan giya, haƙiƙa saɓon Allah. me ya kawo wannan? Amma ba a bincike kuma ba a nemi ilimin abin ba. Amma duk ɗan faira na haƙiƙa ba za ka same shi da kowanne abu ba na saɓon Allah.

 

Su waye kuma ’yan haƙiƙa?

 

Mutane ba su gane wa ne ana so a cutar da Shehi Ibrahim ne a cutar da fairar shi ‘yan haƙiƙar nan ƙananan yara ne jahilai amma har yanzu babu wani Shehi kamili da aka ji ko aka gan shi da wannan aƙida.

 

Mene ne fatanka na ƙarshe?

 

Babban fatana shi ne haɗin kan Musulmi, ni wannan rarrabuwar ba na son ta. Duk wata rabuwa wane ɗan Izala wa ne ɗan Shi’a wa ne ɗan kaza da kaza duk ba zai ci da addinin gaba ba. Ina son na ga waɗanda ba addininmu guda ba su bi addinin Muslunci su fahimci saƙon da Annabi muhammadu (S.A.W) ya zo da shi. Na gode ƙwarai.

 

©Daga jaridar Blueprint Manhaja ✍️.

Share

Back to top button