Tsananin Bin Sunnar ANNABI (S.A.W) Da SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Iri Daya Ne.

Misalin Tsananin Bin Sunnar ANNABI(S.A.W) Da SHEHU IBRAHIM NIASSE(R.A) Yake.

 

Akwai Watarana Da Ya Umarci Babban Jikansa, IMAM HASSAN CISSE(R.A) Ya Ja Sallah, Da IMAM Ya Tashi Yin Sallah, Sai Duk Bayan Fatiha Ya Ɗebo/Tsinto Ayoyi Daga Wata Surah, Sai Ya Biya Yayi Ruku’u,

 

Da Aka Idar Sai SHEHU(R.A) Ya Ce; Idan Zaka Ja Ni Sallah Daga Yau, Ka Min Irin Sallar ANNABI(S.A.W), Idan Ya Ɗauki Surah Sai Ya Dire Ta,

 

Kada Ka Min Irin Sallar Mutan Gari Kaza, a Tsinto Ayoyi, Duk Da Hakan Ba Laifi Bane, Amma Yadda ANNABI Ya Yi Nake So a Min.

 

ALLAH Ya Ƙarawa SHEHU Karama, Ya Bamu Albarkar Masu Albarka, Ameeen.

 

(©️Sabo Ibrahim Hassan).

Share

Back to top button