Tsawon Shekaru Kusan Dari Baisan Wani Abu Wasa Ba Sai Hidimar Addinin Musulunci.

BINCIKE: Duk wasu alamomin da addinin musulunci ya sharɗan ta na zama waliyin Allah Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RA ya cika su.

 

Tsawon shekaru kusan ɗari baisan wani abu wasa ba sai hidimar addinin Musulunci.

 

Allah yana sanar damu cewar waliyan sa basu da tsoro akan gaskiya, kowa ya shaida rashin tsoron Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi wajan tsage gaskiya.

 

Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi alaramma ne mahaddacin Qur’ani mai girma fitaccen mai tafsirin Alqur’ani mai girma ne ya kai shekaru saba’in da ɗaya yana tafsir ya musuluntar da wadanda ba musulmai ba saidai ace dubbanin al’umma.

 

Da’awar Shehu a addinin Musulunci ta zaman lafiya ce da yada Addinin Musulunci cikin hikima da kwantar da hankali ba tare da ɗage ɗagen makamai ba.

 

Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya haddatar da Almajirai fiye da dubu ashirin zuwa yanzu ta hanyar makarantun sa.

 

Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya shiga sahun bayin Allah da idan ka dawwama da zagin su kana iya shiga cikin fushin Allah sabida shi kansa zagin ma fasikanci ne inji Annabi Sallallahu alaihi Wasallam.

 

Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bawan Allah ne da Allah yai masa ni’imar rayuwa, waɗan da suke tare dashi suna cin albarkacin tarayya dashi su ɗaukaka suyi kuɗi masu sukar shi suna samun na cefa ne harma su sanya manyan shadduna da manyan gidaje da motoci.

 

A yanzu dai cikin hukuncin Allah hidimar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi RA ga addinin Musulunci ƙasar Saudiyya ta zaɓi ɗan sa Alhaji Ibrahim matsayin shugaban kungiyar musulman Nijeriya.

 

Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana A’min A’min

Share

Back to top button