WALLAHI WANNAN HUJJAR KADAI TA ISA HUJJAH AYI MAULIDI

A Cikin Suratu Hud(A.S) Bayan ALLAH (S.W.T) Ya Gaya Ma MANZONSA(S.A.W) Labarurrukan Annabawan Da Suka Gabace Shi Da Kuma Irin Gwagwarmayar Da Suka Yi Da Al’ummominsu, Daga Qarshen Surar Sai Ya Ce Masa:-

 

“Kuma Da Yawa Mu Kan Qissanta Maka Daga Labarurrukan Manzanni(wadanda suka gabata), Gwargwadon Yadda Za Mu Tabbatar(Za Mu Qarfafa) Maka Zuciyarka”.

 

(Suratul Hud: 119).

 

Shehu Ibrahim NYASS(R.A) Yake Cewa:-

 

”In Dai Har MANZON ALLAH(S.A.W) Zuciyarsa Zata Qarfafa Idan An Bashi Labarin Annabawan Da Suka Gabata, To Yaya Kuma Mu Na Mu Zuciyoyin Ba Za Su Qarfafa Ba Idan An Karanta Mana Tarihin MANZON ALLAH (S.A.W)???”

 

To Jama’a Idan Muka Kalli Wannan Ayah Da Idon Basira, Ai Ita Kadai Ma Ta Ishe Mu Hujjar Taruwa Ayi Maulidi.

 

Jama’a Maulidin Nan Fa Wallahi Ayyukan Alkhairi Ne Masu ‘Dimbin Yawa a Kunshe a Cikinsa.

 

MISALI:

 

(A) Wa’azi Da Tunatarwa Da Nasihohi Ta Hanya Jiyar Da Al-ummah Tarihin MANZON ALLAH (S.A.W) Da Yakokinsa Da Sauran Gwagwarmayar Da Ya Sha Fama Da Ita Domin Isar Da Saqon Ubangiji(S.W.T).

 

(B) Karatun Al’Qur’ani Da Hadisan MANZO (S.A.W).

 

(C) Rera Yabon Manzon ALLAH(S.A.W) Da Iyalan Gidansa Sahabbansa Wadanda Suka Taimake Shi Wajen Isar Da Sakon Ubangiji (S.W.T).

 

(D) Zikirin ALLAH Da Salati Ga SHUGABA (S.A.W).

 

(E) Shigar Da Soyayyarsa Da Qaunarsa Cikin Zukatan Manya Da Qanqana, Ta Hanyar Fa’dar Siffofinsa Da Halayensa, Da Mu’ujizozinsa(S

.A.W).

 

(F) Taimakawa Juna Cikin Bin ALLAH, Ta Hanyar Zumunci Da Kuma Haduwa Da Juna a Bisa Manufa Guda, Wato Girmama Manzon ALLAH(S.A.W).

 

(G) Ciyarwa Da Shayarwa Fi-Sabilillahi.

 

To ‘Yan’uwa Idan Kuka Dubi Wadannan Abubuwan Da Na Lissafta a Sama Da Ma Wasunsu Wadanda Na Manta Ban Fa’da Ba, Ai Zaku Ga Cewar Dukanninsu Ayyukan Alkhairi Ne Wadanda Musulunci Yake Umarni Da Su.

 

ALHAMDULILLAH!

 

ALLAH KA SANYAMU CIKIN WADANDA IDAN AN TARU ANA KARANTA TARIHIN ANNABI(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA ZUCIYOYINMU SU SAMU NUTSUWA DA FARIN CIKI.

 

YA KARE MU DAGA AFKAWA CIKIN TAWAGAR DA IDAN AN TARU ANA BADA TARIHIN MANZON RAHAMA(S.A.W) DA FADAN DARAJOJINSA SAI SU JI KAMAR ANA ZUBA MUSU RUWAN DALMA A KUNNE, KUMA ZUCIYARSU KAMAR ZATA FASHE DON BAKIN CIKI AMEEEEEN.

Share

Back to top button