Wanda bai hawa dutsen arfa ba, idan ya hau dutsen Dala a ranar takutaha zai samu lada hawa dutsen arfa. – Baba Impossible
RANAR TAKUTAHA:
Wanda bai samu damar hawa dutsen arfa ba idan ya hau dutsen Dala a ranar takutaha za a bashi lada tamkar ya hau dutsen arfa… -Inji Malam Tahar Baba Impossible
Daga A Yau News
Wani fitaccen malami a Kano, Dr. Tahar Baba Impossible tsohon Kwamishinan harkokin addini na jihar Kano, ya ce ranar Takutaha rana ce ta ado da ake kambamata ake yin yanka da dafe-dafen abinci Sarakuna suna yin hawa “da niyyar girmama ranar sunan mazon Allah S.A.W”
A cewar Malamin kamar yadda A Yau News ta ruwaito ya ce takutaha ta samo asali ne tun bayan bayyanar addinin musulunci kuma ana yin bikin ne a ranar sunan Manzon Allah S.A.W,
“A zamanin Shehu Usman Fodio ya jiyo mutanen gari sun fita suna bikin ranar suna ta fadin takutaha sadaka, ta Annabi, da gari ya rude sai Shehu Usman Fodio ya tambayi me ake yi haka sai aka fada masa murnar ranar sunan Annabi ne (S.A.W). Sai ya ce ku tai, taku ta… ma’ana ku tafi, ranar taku ce, to daga nan sai mutane suka tafi suna ta maimaita takutaha, takutaha, takutaha, shikenan sunan ya zauna a haka…” inji shi
Shehun malamin ya cigaba da bayyana cewa “Abubuwa da Hausawa ke yi a wannan rana kusan kamar na ranar Sallar idi ne, sai dai shi wannan an fi yin sadakar abinci a rarraba, sannan malamai suna haɗuwa su yi ta yabon Annabi S.A.W ana basu kudi… wasu sarakunan ma har shirya hawa suke yi, kamar irin su Sarkin Gumel, da Daura da Katsina har suna yin hawa, ana kiransa hawan sallar Gani”
“A yanzu da maulidi ya zo sai ana zuwa dutsen Dala a hau duk ranar takutaha domin cewa aka yi “wanda bai samu dama ya je dutsen arfa ba idan ya hau dutsen dala a ranar takutaha za a bashi lada tamkar ya hau dutsen arfa..