Wani Bawan Allah Ya Ginawa Yan Tijjaniyya Katafaren Madaukakin Baki A Gombe.

Wani Bawan Allah Ya Gina Katafaren Masaukin Baki Wa Yan Darika Fisabilillah A Gombe.
Wannan bawan Allah mai Suna Alhaji Muhammadu Adamu Kashere ya gina kawataccen gida na zamani fisabilillah don sauke baki da suke zuwa daga kasar Morocco da Senegal dama bakin mu na cikin gida najeriya.
Masaukin bakin ya kunshi bangarori daban daban a gidan akwai dakunan kwana da bandaki a kowanne daki, da kuma manyan falo na zamani. Gidan yana kusa da masallacin jumma’a na kungiyar fityanul islam da kuma Makarantar kungiyar dake anguwa uku cikin garin Gombe.
Muna addu’an Allah ya saka masa da alkhairi, ya yawaita mana irin su a cikin al’ummar Musulmai, Allah ya yawaita masa arzikin sa. Amiin.
Daga Babangida A. Maina
Tijjaniyya Media News