Wani bawan Allah ya musulunta a zawiyyar matashin malamin Sheikh Muhammad Shamsuddeen (Young Sheikh) Zaria.

Musulunci Ya Kara Samun Karuwa A Wurin Majalisin Young Sheikh Zariya.

 

Da yammacin ranar juma’a ne, wani bawan Allah ya musulunta a zawiyyar matashin malamin nan Sheikh Muhammad Shamsuddeen (Young Sheikh) dake Tudun Wadan Zariya.

 

Inda matashin ya amshi Musuluncin a hannun Sheikh Abulfatahi Sani Attijani wanda ya zo daga Bauchi ana tsaka da gudanar da majlisi.

 

Idan baku manta ba haka aka yi a baya ma inda wani babban Fasto shima ya amshi addinin Musulunci a zawiyyar ta Young Sheikh dake garin Zaria jihar Kaduna.

 

Alhamdulillah, Allah ya tabbatar dashi a Addinin musulunci ya kara mana kaunar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ

. Amiin

Share

Back to top button