Wani Bawan Allah Yana Tambaya Wai Litattafai Guda Nawa Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA. Ya Rubuta.

Wani Bawan Allah yana Tambaya wai litattafai guda nawa Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi R T.A. ya Rubuta ga Amsar da zamu Bashi.

 

Ilimi daga zuciya yake fitowa baki ya furta sannan sai rubuta kuma lokaci ke Badawa ayi Rubutu shi Shehu ya Shekara 75 Yana Fassara AlQur’ani a tarihin Nijeriya Babu Wani malami daya yayi tafsirin Alqur’ani Cikin harshen Hausa da Fulatanci wacce ta yadu a fadin Africa da Duniya.

 

Sai irin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi R.T.A. a tarihin Nijeriya Sheikh Dahiru Usman Bauchi shi ya fara Tafsiri

 

Babu duba littafi daga shi sai Calbi a hannun sa dashi da Mai jan baki duka da kai suke Karatu Babu dubawa Kuma Tafsirin Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi malamai Sun sani.

 

itace Tafsiri Mafi tsada Cikin TAFSIRAN Wato Qur’ani bil Qur’an maganan Rubuta Tafsiri na Maulana masu sha’awa sunyi nisa wajan Rubuta shi Shehu yace Shi Tafsiran malamai Sun isheshi baya bukatan Nasa amma masu bukata suje su Rubuta bazai hanasu ba.

 

Akwai Doctoci na Iimi daga Jami’an Azhar suna kan Aiki Akai Tafsirin Shehu na malamai ne ba wai na jeka nayi kaba Kuma Babban Jihadi.

 

Shehu yayi ya kafa makarantun Haddan Alqur’ani Mai Girma a fadin Africa sun Kai guda dubi goma Sha daya (11000) Kuma wadannan makarantun duk Shekara sukan fidda mahaddata Qur’ani A kalla mutum dubu biyar zuwa dubu shida.

 

Allah yakara wa Shehu lafiya da Nisan Kwana Alfarman Manzon Allah S.A.W. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Abubakar Ibrahim..

Share

Back to top button