Wani Daga Cikin Sarakunan Magabata Mai Tsananin Adalci Da Tunani, Shi Wannan Sarkin Ba Musulmi Bane.
WANNAN SARKIN YA BURGENI
Wani Daga Cikin Sarakunan Magabata Mai Tsananin Adalci Da Tunani, Shi Wannan Sarkin Ba Musulmi Bane.
Lokacin da yazo mutuwa sai yasa aka kira masa manyan sojojinsa (dogarawansa) sai yace musu, yana son yayi wasu wasiyoyi gudu uku, idan mai yanke kauna (MUTUWA) ta daukeshi.
Wasiyoyin kuwa sune:
1. Likitocin da sukafi kowa kwareya a fadin kasarsa, su yakeso sudauki akwatin gawarsa su fito da’ita bainar jama’a kafin aje a binneshi.
2. Dukkan abin daya mallaka na kudi dana zinari ko azurfa, yana son a tattarasu a watsasu a hanyar daza’a bi da gawarsa zuwa makabarta.
3. Hannayensa kuma yace yana son a barsu a wajen akwatin suna Lilo inda kowa dake wajen zai iya ganinsu (hannayen).
Babba daga cikin sojojinsa sai yayi mamaki game da wayannan wasiyoyi sai ya tambayeshi dalilin da amfanin yin haka sai shi kuma sai yace:
1. Inason likitoci su dauki gawa tane domin na nunawa mutane cewa, idan mutuwa tazo ko da likitocin da su kafi kowa kware wane, baza su iya warkadda mutum ba.
2. Ina son a watsa dukiyata akan hanyane domin mutane su san cewa duk abinda aka samu a duniya, a duniya ake barinsa.
3. Inason a bar hannayena suna rito ta waje ne domin mutane su gane cewa munzo duniya hannu babu komai haka kuma zamu koma hannunmu babu komai.
INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIN RAJI’UN, Shin daga cikin mu wanne ne yake Wannan tunani ?
Hakika Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa; “Bayanai sun tabbata cewa, daga lokacin mutuwa zuwa tsayuwa a gaban Ubangijin Madaudakin Sarki akwai shinge-shinge na azaba kuma karami daga cikin su itace, “MUTUWA”.
Allah ya kara mana kauna da soyayyar Annabi Muhammad S A W. Amiin