Wani Dattijo Ne Jikokin Sa Suka Ce Sunan So Ya Basu Labarin Wanda Yafi Kowa Jarumta a Cikin Al’umma

LABARIN WALIYYI ABJADU

 

 

Wani dattijo ne jikokin sa suka ce suna so ya basu labarin wanda yafi kowa jarumta a cikin al’umma, kuma wanda jarumtar sa ta amfanar dashi da musulmi a duniya da lahira, shine ya basu labarin WALIYYI ABJADU.

 

Tsohon yace, A wata qasa daga qasashen duniya mai suna DAURUL FALAK, an haifi wani kyakkyawan yaro a ranar da rana ta fito bayan hasken wata ya kau, cikin wata daga watannin arabiya wanda tayi daidai da shekara a shekarun miladiyya. Sunan mahaifin yaron KAUKAB, sunan mahaifiyar sa BURUJ.

 

Wannan yaron tun tasowar sa har yakai shekaru 18, bashi da aiki sai wayannan abubuwan:

 

1. Tsantsar tauhidi, kiyaye sallar Farilla sau biyar a jam’i da azumin watan ramadana.

 

2. Karatun kur’ani daidai gwargwado da neman ilimi.

 

3. Koyi da sunnonin Annabi SAW da kuma kokarin biyayya ga iyaye bisa umurni da hani.

 

Mutanen garin suna qaunar sa sosai har suke masa laqabi da ABJADUL ISLAM. Bayan ya shekara 18 sai yayi mafarki da wani balarabe, yace masa sunana BADDU (بط) ina so ka shiga duniya domin neman yardar Allah ta hanyar koyi da bayin sa waliyai.

 

Yana farkawa ya nemi iznin iyayen sa ya shiga duniya, sai yaje wata qasa a qasashen yamma, ya gamu da wani waliyyi ana kiran sa KHATMUT TIJJANI. Ya nemi iznin zama dashi sai yace masa “maraba da zuwa Abjadu, ai nasan da zuwan ka, toh ni dai bani komai sai abubuwa guda uku, amma duk wanda ya riqe su sai ya shiga aljanna ko baya so, sune”:

 

1. Istigfari 100, Salatil Fatihi 100, Hailala 100 bayan sallar asuba da na la’asar.

 

2. Istigfari 30, Salatil Fatih 50, hailala 100, jauhara 12 sau daya a rana kullum.

 

3. La ilaha illallah ba adadi ranar juma’a bayan sallar la’asar gabanin faduwar ranar har magariba.

 

Wannan saurayin yace zai iya, waliyin nan yace toh naji amma akwai sharadi, dole ka daina neman madadin wani waliyyi in ba ni ba, ba zaka hada wannan wuridin da wuridin wasu waliyai ba, ba zaka daina yin wannan wuridin ba har mutuwa, saurayi yace da himmar ka maulana an gama. Waliyin nan yace to daga yau sunan ka ABJADUL IMAN.

 

Haka saurayin nan yayi ta kokarin kiyaye wuridin nan daidai gwargwado har ya shekara 40, a lokacin sai khatmut Tijjani yace masa yanzu ka kai muqamin da zan turaka wurin babban da na, in kaje zai maka aure bayan ka tsallake ayyukan da zai saka ka.

 

Kwanci-tashi sai ABJADUL IMAN ya isa garin da khatmut Tijjani ya labarta masa amma sai an tsallake wani teku ake isa garin. A bakin tekun an rubuta SUNAN WANNAN TEKUN FAIDA, TAKA DA QAFARKA KA WUCE IN AN MAKA IZNIN ZUWA. Ai kuwa Abjadu sai ya fara taka ruwan nan bai nitse ba, amma yana zaton zai dade bai kai tsakiyar ruwan ba, sai yaga taku 7 ya kaishi garin dake tsakiyar ruwan, an rubuta BARKA DA ZUWA GONAR ARUFAI.

 

Bayan ya shiga sai ya ga jama’a kowa ya shagala da kanshi, babu mai magana da wani, Yana isa fadar garin sai ya shiga ya miqa takarda, aka kaishi wurin Sarki wanda shine babban yaron khatmut Tijjani. Yayi masa maraba sannan yace masa, zan maka aure amma sai ka tabbatar min da cewa za ka iya riqe mata. Shiga ga daki can ka dinga karanta abinda ka gani a jikin bangon dakin har sai ka fahimci yadda ake noma ba tareda fartanya ko galma ba, da yadda ake mutuwa ba tareda an daina numfashi ba.

 

Bayan dan lokaci, Abjadu ya zo gun sarki da amsoshi gamsassu, sarki yace lallai yanzu kam ka cancanci aure, zan aura maka mata biyu a lokaci daya, kuma sunan ka ya zama ABJADUL ISHAN daga yau. Saurayi yayi godiya, aka daura masa aure da mace biyu, ta farko sunan ta BARA’ATU, ta biyu sunan ta FANAITU.

 

Alhamdulillah! Yara kunji labarin waliyyi Abjadu wanda yafi kowa jarumtaka da amfanuwa tareda amfanarwa. Iznin fita neman ilimin a farko Annabi yayi masa, na biyu Shehu Tijjani yayi masa, a qarshe kuma ya samu damanar Shehu Ibrahim akan FA ASGARU ATBA’IY BARI’UN MINASH-SHIRKI wato har abada ba zai yi shirka ba, kuma FA ASGARU ATBA’IY UNILU FANA’A wato ya samu qarewa cikin zatin Allah.

 

Wannan labarin bushara ne ga dukkan batijjane, da iznin Annabi ka sadu da Shehu Tijjani, da iznin Shehu Tijjani ka sadu da shehu ibrahim, saduwa da Shehu ke tsallakar da mutum daga sharrin duniya amma in ka yi tarbiyatul azkar bayan zuciyar ta cika da sadiqar soyayya da hidima gareshi.

 

Mu qara riqe abubuwan da muke kai, wallahi a yau mu Allah yake dubawa yake saukar da rahmar sa, fushin sa ga halittu kuma domin mu yake Afwa, mune nashi, mune masoyan shi, mune bayin sa na haqiqa.

 

Allah kayi tsira da aminci ga Annabi Muhammad, ka ninka yardar ka ga katimul wulaya, ka cigaba da daukaka sunan sahibul faida.

 

✍ Sidi Sadauki.

Share

Back to top button