Wani Mutum Daga Niger Delta Ya Tura Tambaya Gun Shehi RTA Akan Hukuncin Kwallon Kafa a Addini.

Kwallon Kafa (Football)

 

Wani Mutum mai suna Malam Yusuf Ango daga Niger Delta ya tura tambaya gun Shehi RTA akan Hukuncin Kwallon Kafa a Addini.

 

Ga abinda Shehu RTA yace: Ai shi Kwallo hanyace ta koyan yaqi. A zamanin da akanyi wasannin gudu da tsalle-tsalle, harbi, shad’i da kokuwa da sauransu duk don akoyi yaqi, Duk wanda ya iya gudu idan yaqi ya kaure zai gudu, duk wanda yafi iya harbi idan yaqi yazo lokacin harbi sai yayi, duk wanda yafi iya kokuwa idan yaqi yazo babu makami sai yai amfani da basiran kokuwansa wajen yin yaqin.

To saidai a wannan zamani din ana yaqinne da injuna shiyasa amman Kwallo hanyan ce ta koyan yaqi din.

 

A makaranti damuke dasu guda uku:

1. Makarantar Qur’ani

2. Makarantar Ilmin Addini da

3. Makarantar Boko

Idan antashi daukan aikin Force(damara) baza aje tafarko ko tabiyu ba saidai ta uku.

Suwaye yan Kwallon??

Sune Yan Boko.

Towai idan ance suma karsuyi Kwallon idan wani abun tsoro ya tunkaromu suwaye zasu zamo masu karemu, tinda babu Wanda ya koyi harkan yaqin??

 

A zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam anzo ana daukan sojojin yaqi sai akacire wani mutum sai yafara kuka sai aka tambayeshi dalili sai yace; Ya Rasulallah SAW wai ance ban chanchanta inje yaqi ba kuma andauki wane bayan duk randa mukai kokuwa saina kayar dashi akasa🤔.

 

Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace to kuzo kuyi agabana ingani da sukai sai ya kayar dashi kamar yadda ya fad’a, sai Annabi SAW yace lallai ka chanchanta kashiga kaima.

 

Maulana RTA ya kara da cewan Sai dai shi mai Kwallo agaya masa kar yayi wasa da Sallah, idan lokacin Sallah yayi tofa yai Sallah kamun yatafi kwallonsa.

 

Allah karawa Shehu RTA lafiya da Tsawon Rai albarkar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam A’min A’min

Share

Back to top button