Wani Ya Tambayi ANNABI (S.A.W) Cewa:”Ya RASULULLAHI! Ta Yaya Zan Samu Tsira a Wajen ALLAH ?

Wani Mutum Ya Tambayi MANZON ALLAH (S.A.W) Cewa:”Ya RASULULLAHI! Ta Yaya Zan Samu Tsira a Wajen ALLAH???”

 

Sai MANZON ALLAH (S.A.W) Ya Ce Masa:”KAR KA YAUDARI ALLAH”

 

Sai Ya Ce”Ta Yaya Ake Yaudarar ALLAH???”

 

Sai ANNABI (S.A.W) Ya Ce Masa:”Shi Ne Ka Aikata Wani Aikin Da ALLAH Ya Umurceka, Amma Da Niyyar Neman Yabo a Wajen Wanin ALLAH, Ka Ji Tsoron Riya. Domin Ita Ce ‘Karamar Shirka, Hakika a Ranar Alkiyama a Gaban Dukkan Halittu Za’a Fito Da Mai Yin Riya, Za’a ‘Kira Shi Da Sunaye Guda Hudu:

 

*1. YA KAI MAI YIN RIYA!

*2. YA KAI MAYAUDARI!!

*3. YA KAI FAJIRI!!!

*4. YA KAI MAI ASARA!!!!

 

Ayyukanka Sun Ta6e!

Kuma Ladanka Ya Zube!!

Baka Da Lada Anan WajenMU!!

 

Jeka Ka Kar6o Ladanka a Wajen Wadancan Da Kake Yi Domin Su Yabe Ka! Ya Kai Mayaudari!!”.

 

(KITABUL KABA’IR Na Imamuz Zahaby, Shafi Na; 9).

 

YA ALLAH! KA ‘KARA KARE MU DA ZURI’ARMU BAKI ‘DAYA, DON ALFARMAR SAYYIDUL-WARA (S.A.W) AMEEEEEN.

Share

Back to top button