Wani Zamani Zai Zoma Al’ummata Duk Wanda Yariqe Addininsa Zai Zama Kamar Yariqe Garwashin Wuta.

ANNABI (S.A.W) Yace:

 

Akwai wani zamani zai zoma al’ummata (acikinsu) duk wanda yariqe addininsa zai zama kamar wanda yariqe garwashin wuta.

 

ANNABI (S.A.W) yace: Nan gaba kadan al’ummomi zasu zagayeku (ku musulmai) kamar yadda jama’a ke zagaye kwanon abinci.

 

Sai sahabbai suka tambayi ANNABI S.A.W cewa: Shin bamu da yawane a lokacin ?

 

Sai ANNABI S.A.W yace: kuna dayawa amma yawanku taron tsintsiyane babu

shara kuma nan gaba kadan Allah (S.W.T) zai cire kwarjinin da kuke dashi acikin zukatan abokan gabarku (kafirai) kuma yasanya muku rauni.

 

Sai yace son duniya da qin mutuwa.

 

ANNABI (S.A.W) yace: “Wasu shekaru masu yaudara za suzo wayanda acikinsu zakaga ana qaryata mai gaskiya kuma ana gasgata mai karya.

 

Mai ha’inci zaiyi zamansa cikin kwanciyar hankali, amma za’a riga cutar mutumin kirki.

 

‘Yan uwa yanzu a wane irin yanayi muke ciki ?

 

Tofa in baka sani ba Yakamata ka sani saboda Munzo lokacin a halin Yanzu

 

ALLAH YASA MUGAMA DA DUNIYA LAFIYA Bijahi S.A.W. AMEEEEEEEEN

Share

Back to top button