WASIYAR MAULANA SHEHU ALIYU HARAZIMI HAUSAWA KANO (RTA).

WASIYAR MAULANA SHEHU ALIYU HARAZIMI HAUSAWA KANO (RTA).

 

A ranar da Shehu Harazimi (R.A) zaiyi wafati bai wuce saura awa daya ba (1hr) ya canja siffa zuwa ga Allah (T) yake cewa; “Ku riqe wadannan abubuwa a tsawon rayuwarku.

 

1- Ku riqe La’ilaha Illallah

2- Ku Kula da Sallah.

 

3- Ku riqe ‘Dariqar Tijjaniyya

4- Ku riqe Alqur’ani.

 

5- Ku riqe Hadisai na SHUGABA (Sallallahu Alaihi Wasallam)

6- Kuyi riqo da Haquri.

 

7- Kar ku kula da Duniya domin Duniya hatsari ce.

 

Shehu (R.A) ya cigaba da cewa; “LA’ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULULLAH” ya ringa maimaitawa har wadanda suke wajen suka rude da zikirin “La’ilaha ilallah”, basu ma san lokacin da Shehu (R.A) yayi wafati ba, kawai shurunsa sukaji…

 

Allah ubangiji madaukakin sarki ka kara yardar ka ga Shehu na Hausawa mai tamburan Zikiri da Salatin MA’AIKINA (Sallallahu Alaihi Wasallam). Amiin 🤲

Share

Back to top button