Wasu Makiya Sun Hana Sheikh Dahiru Bauchi RA Taron Yiwa Kasa Addu’a A Birnin Abuja.

ALLAH Bazai Basu Nasara Ba.

 

Wasu makiya Shehu sun sanya ministan Abuja ya hana Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA yin taron addu’an zaman wanda aka shirya gabatar wa a filin Old Parade Ground dake Area 10 a birnin tarayya Abuja.

 

Ba muyi mamakin yadda gwamnonin suka aikatawa Maulanmu Shehu Dahiru haka ba, don a cikin su ya taba hana almajiranci a jihar sa tare da kwashe dukkanin almajiran zuwa gidajen su baki daya. Insha Allah Allah bazai basu nasara akan Lisanul Faidah ba.

 

Mun samu sunayen hakikanin mutanen da suka hana Maulana Sheikh Dahiru Bauchi gudanar da gagarumin taron yiwa kasa addu’an zaman lafiya da kuma Allah ya zaba mana shugabanni nagari a tarayya Najeriya.

 

Zamu fito da sunayen su, Idan halin hakan ya tabbatar daga Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun Sayyadi Alhaji Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi RA.

 

Daga baya mai alfarma sarkin Musulmai ya bada umurnin a bude babban Masallacin Juma’a dake Abuja don Sheik Dahiru Bauchi ya gudanar da taron sa na addu’a ga najeriya.

 

Allah ya cigaba da kiyaye Maulana Sheikh Dahiru Bauchi RA da kariyar sa. Amiiiin Yaa Allah

 

ALLAH yana maganin su ya kare Maulanmu Sheikh Dahiru Bauchi ya kara masa lafiya da nisan kwana albarkacin Manzon Allah. Amiiiin

 

Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button