Wasu Muhimman Kalamai Da ANNABI Muhammad (S.A.W) Ya Fada A Kan Mata.
GARE KU MATA!
Wasu Muhimman Kalamai Da ANNABI (S.A.W) Ya Fada A Kan Mata.
Annabi (SAW) Ya ce: ” Ita mace ba ta kasancewa mafi kusanci ga mahaliccinta (a wani wuri) fiye da cikin gidanta.” [Silsilatus-sahiha 2688]
Annabi (SAW) Yace: ” Duk macen da ta shafa turare, sai ta wuce wasu mutane don su ji kamshin (jikinta) to ita mazinaciya ce.” [Sahihu sunanin Nasa’i 5141]
Annabi (SA W) Yace: ” Duk macen da tasa turare ta fita zuwa Masallaci, baza’a amsa mata Sallar taba har sai tayi wanka.” [Silsilatus sahiha 1031]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Duk wanda ALLAH ya azurta shi da mace tagari, hakika ALLAH ya taimake sa da rabin addini, sai ya kiyaye dokokin ALLAH wajen samun sauran rabin addininsa.” [Sahihut Targheeb-1916]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Duk matar da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba, to haramun ne ta ji kamshin aljanna.” [Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209)
Annabi (S.A.W) Yace: ” kada wata mata ta bayar da izinin (shiga) gidan mijinta, alhali yana nan, sai da yardarsa. [Muslim 1026]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Mutane biyu sallar su ba ta wuce kawunan su:
1. Bawan da ya gujewa mai gidansa har sai ya dawo.
2. Matar da take sabawa mijinta har sai ta daina.” [Sahihut targib 1948]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Mace ba za ta taba sauke hakkn ALLAH ba har sai ta sauke hakkin mijinta gabaki daya.” [Sahihut targib 1943]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Da a ce zan umurci wani ya yi wa wani sujjada, to da na umurci mace ta yi wa mijinta sujjada.” [Sahihut targib] [160]
Annabi (S.A.W) Yace: ” ALLAH baya kallon matar da bata godewa mijinta, kuma bata wadatuwa da shi.” [Sahihut targib 289]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Ku saurara, Ashe bana ba ku labarin matan ku ba a cikin aljanna? (sai yace): “Ita ce mai soyayya kuma mai haihuwa. Idan ta yi fushi ko aka saba mata, ko kuma mijinta ya yi fushi sai ta ce masa: wannan shine hannu na a kan hanunka, ba zan kifta ido ba har sai ka yarda.” [Sahihut targib 1941]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Matar da take kwaikoyon maza ALLAH Ya La’ance ta.”
[Ahmad 2/325, Abu dawud 4098-4099]
Annabi (S.A.W) Yace: “Akwai wasu mutane guda 2 jinsin su na ‘Yan wuta ne sai dai bai taba ganin su ba .Da kuma mata ga sutura a jikin su amma da su da tsiraici daya suke, karkatattu masu karkatarwa, kawunan su kamar tozon rakumi, ba za su shiga aljanna ba ko kamshin aljannar ba za su ji ba, kuma kamshin Aljanna ana samunta daga wuri kaza zuwa wuri kaza.”[Muslim 2128] [164]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Duk matar da ta cire suturar ta agidan da ba gidan mijinta ba, ta qeta hijabin da ke tsakaninta da ALLAH mabuwayi mai d’aukaka.” [Imam Ahmad 6/199, 267, Hakeem cikin Mustadaraka 4/288]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Kuji tsoron duniya sannan kuji tsoron mata, domin farkon fitinar bani Isra’ila ta kasance daga mata ne.” [Muslim 2742]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Ana auren Mata da abubuwa guda 4: Don dukiyarta, don kyawunta, don nasabarta, don addininta, na hore Ku da Ku auri ma’abociya addini saboda zaku ribantu da ita.” [Muttafaqun Alaihi]
Annabi (S.A.W) Yace: “Mafi alkhayrin jindad’in duniya, shine ka samu Mace Saliha.” [Muslim)
Annabi (S.A.W) Yace: “Idan mace ta sallaci lokaci biyar, ta yi azumin watan Ramadan, kuma ta kiyaye farjinta kuma ta yi biyayya ga mijinta, ta shiga Aljannah.” [Rawahul Bazzar]
Annabi (S.A.W) Yace: “Mace Saliha idan ka yi duba gareta sai ta debe maka kewa idan ka buya gareta sai ta kiyaye kanta.” [Alhadith]
Annabi (S.A.W) Yace: ” Ya taron Mata Ku yawaita sadaka kuma Ku yawaita neman gafara, domin lallai na ga kun fi yawa a cikin wuta” sai wata mace daga cikin su ta ce: Me muka aikata Ya Manzon ALLAH muka zama mafi yawanmu ma’abota wuta? Sai Manzon ALLAH (S.A.W) Yace: ” kuna zagi sannan kuma kuna kafurcewa (butulcewa).
Allah yasa mu dace Albarkan ANNABI S.A.W. Amiiiin Yaa ALLAH