Wasu Sojojin Najeriya Sunyi Sanadiyar Mutuwan Dan Agaji Fityanul Islam Of Nigeria Dake Jihar Kaduna.

INNALILLAHI WA’INNA’ILAIHI RAJI’UN.

 

….Allah ya yiwa Dan Agaji Fityanul Islam Ibrahim Admin rasuwa dake Jihar Kaduna.

 

Bayan Lokacin Da Ake Gudanar da Bikin Yayanshi da Kanwarsa Wani Soja Yazo Wucewa Kuma ta Inda Ake Taron Biki, Al-hali Kuma Babu Hanyar Dashi Sojan Zai wuce Mai makon Yadanyi Hakuri Abude masa Hanyar Sai Ya nuna Bachin Rai. Bayan Ya samu Hanya Yawuce, Bayan Wani dan Lokaci Sai Sojoji Suka zo Suka Kama Bin Mutanen da Wannan Biki Yashafa Suka Raunata Wasu.

 

Bayan Haka Sai Suka Bibiyi Ibrahim (Admin) Wato Dan Uwan Ango, Har gida Suka Masa Dukan Kawo Wuka Kamar Yadda Kuka.

 

Ibrahim Admin Dan Agajin FITYANUL ISLAM Ne Reshen Jihar Kaduna Karamar Hukumar Rafin Guza Ibrahim Admin Babu Wani Laifi Da Ya’aikatawa Wanda ya Cancanci abunda aka aikatamasa

 

Wanda Suka Samu Rauni Da Wanda suka rasa ransu acikin wanna aika aika, “Ubangijin Allah” Kabi musu kadi Idan Gomnatin Kasa nan Bata Bi musu Kadi ba Akan Wannan Zalinci, Ameen Ya Allah.

 

Bayan Haka Muna Kira Ga Gomnatin Kasannan Da Tabi Kadin Wannan Zalinci da Aka aikatawa Ibrahim (Admin) Wanda yake karamar Hukumar Rafin Guza.

 

“Ubangijin Allah Ya jikan (Ibrahim Admin) da Rahama, “Ubangijin Allah” Ya tona Asirin Wanda Suka aikata Wannan Mummunan Aikin Da Allah Bayaso, “Ubangijin Allah” Yasa Aljanna ce Makomarsa, Allah Yasa Mu cika Da kyau Da Imani Alfarmar Sayyidil Wujudi Annabi Muhammadu (Saw). Amiin

Share

Back to top button