WASU TAMBAYOYI DA AKA YIWA FARFESA IBRAHIM MAKARI (H) DA KUMA AMSOSHINSU

WASU TAMBAYOYI DA AKA YIWA PROFESSOR IBRAHIM MAKARI (H) DA KUMA AMSOSHINSU

 

…..Yaa Sheikh mene ban-banci tsakanin NAFSU da RUHU da QALBU?

 

Akwai_littafi_da Imamu Ghazali ya wallafa akan wadannan, amma dai dukansu sukanzo da maana kusan daya, idan an nufi janibin shaawa da soye soyen rai sai a ce mata Nafsu, idan an nufi janibin sabanin gangan jiki sai a ce Ruuh, idan an nufi qudurce qudurce sai a ce Qalb. Wannan amsar ba zata gamsar daga komawa zuwa ga littafai ba.

 

Mai bada amsar ma ya taba yin Majlisi akan raino da yaye a hanyar Allah, yayi magana mai dan tsawo akan wadannan. (A iya neman Cassette)

 

Don Allah Malam, ina neman ingancin wannan Hadisin:

في حكمة مجامعة النساء وهي

وصية النبي صلى الله عليه وسلم لعلي بن أبي طالب رضي الله عنه قال النبي :

:

Acikin hikmar Saduwa Da Maata, Kuma wannan wasiyya Ce Da Daga Manzon Allah saw Zuwaga Sayyidna Aliyu bn Abi Dalib rta.

:

يا علي لا تجامع المرأة في نظر النجوم فإذا كان فيه الولد يكون كاذبا.

:

Ya Aliyu kada ka sadu da iyalinka acikin KALLON taurari (wato a sararin samaniya) Idan Aka Samu ciki a wannan Saduwa to zai kasance maqaryaci.

:

ولا تجامع المرأة في حيضها فإذا كان فيه الولد يكون أبرص وأجذم.

:

Kada ka sadu da MACE a lokacin haila, idan Allah swt Ya Hukunta samun ‘Da to zai kasance da cutar kuturta.

:

ولا تجامع المرأة والناس يسمعون صوتها فإذا كان فيه الولد يكون سفيها.

:

Kada ka sadu da MACE alhalin mutane suna Jin sautin ta, idan Allah swt Ya Hukunta samun ‘Da to zai kasance Wawa ko gaula ko ga’bo.

:

ولا تجامع المرأة وقت الضحي والنهار فإذا كان فيه الولد يكون مجنونا.

:

Kada ka sadu da MACE a lokacin hantsi ko kuma da Rana tsaka, idan Allah swt Ya hukunta samun ‘Da to zai kasance Mahaukaci.

:

ولا تجامع المرأة وهي تنطر النجوم فيكون الولد عاصيا لله ورسوله.

:

Kada ka sadu da MACE alhalin tana KALLON taurari a sama, idan Allah ya hukunta samun ‘Da to zai kasance mai Sabon Allah da Manzon SA.

:

ولا تجامع المرأة وهي كارهة فيكون الولد عاقا لوالديه.

:

Kada ka sadu da MACE Akan tilas, idan Allah ya hukunta ‘Da to zai kasance mai rashin biyayya Ga mahaifansa uwa da UBA.

:

ولا تجامع المرأة وأنت تنطر فرجها فيكون الولد أعمي.

:

Kada ka sadu da MACE kana mai KALLON farjinta, idan Allah ya hukunta ‘Da to zai kasance Makaho.

:

ولا تجامع المرأة ليلة الأضحي ويومها فيكون الولد سفاك الدماء.

:

Kada ka sadu da MACE daren Babbar sallah da kuma ranar ta, idan Allah ya Hukunta ‘Da to zai zamo Dan Ta’ adda mai zubar da jini.

:

ولا تجامع المرأة آخر الأربعاء من الشهر فيكون الولد عدوَّ الله و النبي والمسلمين

:

Kada ka sadu da MACE a larabar karshen ko wane wata na Musulunci, idan Allah ya Hukunta ‘Da to zai zamo maqiyin Allah da Manzon Allah da kuma Musulmi baki daya.

:

AMSA: Wannan hadisin Kagagge ne!

 

Shehi, ina aikin bautar kasa NYSC a kudu, makarantar da nake koyarwa suna da tsarin gabatar da addu’a ranar Juma’a da Litinin, dukansu Kiristocine ni kadaine Musulmi. Ya halatta na rinka shiga anayin addu’o’in nasu dani?

 

Bai halatta ka shiga cikin Adduan da ka tabbata za a yi Shirka da Allah cikinsa ba, amma idan ana gudun wata fitina a Addinin Mutum babu laifi ya shiga a Zahiri amma a Zuciyarsa yana qudurta qin hada Allah da waninsa.

 

Ya ingancin hadisin da ake cewa Maaiki SAW yace Wanda yayi bushara da zuwan Ramadan wuta ba zata ci shi ba? Shin ya halatta afadi labarin zuwansa?

 

Kuskure ne danganta wa Manzon Allah (SallallLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) wannan maganar; domin bai fada ba…

 

Sannan ana tabbatar da tsayuwar watan Ramadhan ne a ranar 29 ga watan Sha’aban kaman yanda shari’ar Musulunci ta tanadar.. Zai yiwu a ga wata a ranar, zai kuma yiwu wata ya ki bayyana ta yanda sai an cika kwanaki 30..

 

Saboda haka a guji yada wannan sanarwa mai cike da kuskure.. Akwai kuskuren danganta wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) abin da bai fada ba, ga kuma kuskuren lissafin wata na al-qamariyya..

 

Allah shi ne masani na hakika.

 

Shin yaya niyyar azumin nafila take, shin idan mutum baiyi niyyar azumin ba har alfijiri ya keto, shin zai iya cigaba da azuminsa?

 

Babu wata ibada da take inganta ba tare da niyya ba, ita kuma niyya wurin ta na asali shi ne zuciya.

 

Hadisi ya inganta daga Sayyiduna RasululLahi (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) yana cewa: ((Duk wanda bai kwana da niyya ba ba shi da Azumi..)) ; saboda wannan magana ta Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) ya sa malamai suka tafi akan rashin ingancin Azumi na farilla da ba a daura masa niyya ba..

 

Akwai kuma wani Hadisin da yake nuna cewa Sayyiduna Rasulullah (SallalLahu alaiHi wa Alihi wa sallam) a wata rana ya wayi gari babu abin karyawa a gidansa, sai kuwa ya ce ai sai mu cigaba da Azumi, ma’ana dai sai bayan alfijir ya dauki niyyar yin Azumin, amma dai wannan a Azumin nafila ne, saboda haka malamai suka ce zai yiwu a yi Azumi na nafila ba tare da an kwana da niyya ba..

 

Amma dai dole shi ma a dauri niyyar a lokacin da aka yi shirin dauka, ma’ana mutum ya kudurce a zuciya cewa zai yi ibadar Azumi ta nafila.. Allah ya karbi ibadun mu

 

Inaso Prof. Yadanyi tsokaci akan mas’alar gaisawa da mace (wadda ba muharramarka ba).

 

Haramun ne a mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya mudlakan, sawa’un macen tsohuwa ce ko budurwa, a mazhabar Hanafiyya da Hanbaliyya kuma haramun ne idan macen budurwa ce, amma ya halatta idan tsohuwa ce wadda ba a shalawarta..

 

Allah shi ne masani na hakika. Ameeeen

Share

Back to top button