Wata Rana Abdullahi Bn Salam(‘Daya Daga Cikin Yahudawan Madina) Ya Zo Wajen MA’AIKI (S.A.W) Ya Ce Da Shi:
Wata Rana Abdullahi Bn Salam(‘Daya Daga Cikin Yahudawan Madina) Ya Zo Wajen MA’AIKI(S.A.W) Ya Ce Da Shi:”Na Zo Ne Domin Na Yi Maka Wasu Tambayoyi Guda Uku(3) Wadanda Babu Wanda Ya San Amsarsu Idan Shi Ba Annabi Bane:
1. Shin Menene Farkon Sharadin Tashin Al-Qiyama???
2. Shin Menene Farkon Abincin Da ‘Yan Aljannah Zasu Ci???
3. Shin Menene Yasa Wani Lokaci Idan Aka Haifi Yaro Ya Kan Yi Kama Da Ubanshi, Wani Lokacin Kuma Uwarshi???
Sai ANNABI(S.A.W) Ya Ce Da Shi:”Yanzun Nan Mala’ika Jibrilu(A.S) Ya Zo Ya Bani Labarin Amsoshin Tambayoyin Nan Naka”.
Sai Bn Salaam Ya Ce:”Mala’ika Jibrilu???”
ANNABI(S.A.W) Ya Ce:”Eh”
Bn Salam Ya Ce:”Ai Mala’ika Jibrilu Shi Ne Makiyin Yahudawa”.
Sai ANNABI(S.A.W) Ya Karanto Masa Wannan Ayar Da Take Cewa:”Man Kana Aduwan Lillahi Wa Mala’ikatihi Wa Jibrila Wa Minkaila Fa’inallaha Aduwan Lilkafiriin”.
Sannan Ya Bashi Amsoshin Tambayoyin sa Kamar Haka:
1. Farkon Sharadin Tashin Qiyama Wata Wuta Ce Wacce Zata Koro Mutane Tun Daga Inda Rana Take ‘Bullowa Har Zuwa Inda Take Fad’uwa
2. Farkon Abincin Da ‘Yan Aljannah Zasu Ci Shi Ne Hantar Wani Kifi,
3. Idan Maniyyin Namiji Ya Riga Na Mace Sauka, To Sai Yaron Ya Zama Yana Kama Da Shi(Uban), Idan Kuma Na Macen Ne Ya Riga Sauka, To Sai Yaron Yayi Kama Da Ita(Uwar).
Daga Wannan Lokacin Sai Abdullahi Bn Salam Wanda Ada Shi Ne Mafi Alkhairin Yahudawa Kuma ‘Dan Shugaban Yahudawan Ya Ce:”Na Shaida Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Haqiqa Kai MANZON ALLAH Ne,
Ya RASULALLAHI! Haqiqa Yahudawa Mutane Ne Masu ‘Kage Da Sharri Ne, Idan Suka San Cewa; Na Musulunta Tun Kafin Ka Tambaye Su Game Da Ni, To Tabbas Zasu Yi Min Sharri Da ‘Kage”,
Da Sauran Yahudawan Suka Zo Sai MANZON ALLAH(S.A.W) Ya Tambaye Su Cewa:”Shin Menene Matsayin Abdullahi Bn Salaam a Cikinku???”
Sai Suka Ce:”Shi Ne Mafi Alkhairin Cikinmu, Kuma ‘Dan Gidan Mafi Alkhairin Cikinmu, Kuma Shi ‘Dan Shugabanmu Ne”,
ANNABI(S.A.W) Ya Ce:”Shin Yaya Kuke Gani Idan Shi Ya Musulunta???”
Sai Suka Ce:”ALLAH Ya Tsare Shi Ba Zai Ta6a Musulunta Ba”.
Jin Hakan Ke Da Wuya Sai Abdullahi Bn Salaam(R.A) Ya Fito Daga Inda Yake ‘Boye Ya Ce:”Ash-Hadu An La’Ilaha Illallahu Wa Anna Muhammadur Rasulullahi”.
Daga Jin Hakan Sai Yahudawan Suka Ce:”Ai Wannan Shi Ne Mafi Sharrin Cikinmu Kuma ‘Dan Gidan Mafi Sharrin Cikinmu”.
Sai Bn Salaam(R.A) Ya Ce:”Ya RASULULLAHI! Ka Ga Abin Da Nake Tsoro Kenan Tun Farko; Sharrin Bakinsu”.
Sayyiduna Abdullahi Bn Salam(R.A) Ya Musulunta Kuma Musulunci Yayi Armashi Sosai Harma Ya Kasance ‘Daya Daga Cikin Malaman Sahabban ANNABI (S.A.W).
Ya ALLAH! Ka Yi Dadin Tsira, Sallama Da Salati Ga Mijin Khadija Angon A’isha, Abul Qaseem Abban Fatima, Wanda Ka Aiko Shi Domin Ya Kasance Rahama Ga Dukkan Talikai.
ALLAH YA ‘KARA MANA SOYAYYAR SHI(S.A.W) AMEEEEEN.