Wata Rana SAYYIDUNA UMAR (R.A) Ya Kai Ziyara Raudhar MANZO (S.A.W) Sai Ya Samu Wani Balarabe Ya Tsaya a Gaban Kabarin Manzon Allah SAW.

Wata Rana SAYYIDUNA UMAR (R.A) Ya Kai Ziyara Raudhar MANZO (S.A.W) Sai Ya Samu Wani Balarabe Ya Tsaya a Gaban Kabarin Yana Addu’ah, Sai SAYYIDUNA UMAR (R.A) Ya Tsaya a Bayansa Yai Shiru Yana Sauraronsa.

 

Balaraben Yana Cewa

 

“Ya ALLAH! Wannan Masoyinka Ne(Yana Nufin MANZON ALLAH), Ni Kuma Bawanka Ne, Shaidan Kuma Makiyinka Ne.

 

Idan Ka Yi Min Gafara, Masoyinka Zai Ji Dadi,

 

Bawanka Zai Rabauta,

 

Makiyinka(Shaidan) Zai Yi Bakin Ciki.

 

Idan Baka Min Gafara Ba, Masoyinka Ba Zai Ji Dadi Ba,

 

Makiyinka Zai Ji Dadi,

 

Bawanka Ya Halaka.

 

Ya ALLAH! Kai Ne Mafi Girma Kar Ka Baqantawa Masoyinka, Ka Yardar Da Maqiyinka, Ka Halakar Da Bawanka, Kafi ‘Karfin Haka Ya ALLAH!

 

Hakika Karimai a Cikin Larabawa Idan Shugaba Daga Cikinsu Ya Mutu Sai Su ‘Yanta Bayinsu a Gaban Kabarin Shugaban Nasu.

 

Wannan Kuma Shi Ne; SAYYIDIL-ALAMINA, Gashi Ya Komo Zuwa Gare Ka.

 

Don Haka Ya ALLAH! Ka ‘Yanta Ni Daga Wuta a Gaban Kabarinsa!”,

 

Sai SAYYIDUNA UMAR(R.A) Yai ‘Kira Da ‘Karfi Ya Ce:

 

“ALLAH Nima Ina Rokonka Da Abin Da Wannan Balaraben Ya Roke Ka!”

 

Sai SAYYIDUNA UMAR(R.A) Ya Fashe Da Kuka a Gaban Kabarin Har Sai Da Gemunsa Ya Jiqe Da Hawaye.

 

Ya ALLAH Muma Muna Rokonka Da Abin Da Wannan Balaraben Ya Roke Ka, Ka ‘Yanta Mu Daga Wuta, Da Iyayenmu Da Matayenmu Da ‘Ya’yanmu Da Duk Wanda Yake Da Haqqi Akanmu Ya ALLAH! Amiin

 

Daga: Sidi Kabir Yola

Share

Back to top button